Rundunar yan Sandan Nigeria ta gano masu shirya zanga-zanga irin ta Kenya a ƙasar

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya ce bayanan sirri da rundunar ta samu sun nuna cewa akwai wasu yan kasashen waje da ke da hannu wajen shirya zanga-zangar da za a yi a fadin kasar.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja ranar juma’a,, Egbetokun ya bukaci daukacin ‘yan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan tare da yin tunani sosai kafin su shiga zanga-zangar.

Talla
Talla

Egbetokun ya ce, “Mun sanya ido kan abun dake faruwa game da shirin yin zanga-zangar. Mun gano wasu kungiyoyi na kira da ayi zanga-zangar tarzoma, suna bukatar ayi irin abun da aka yi a kasar Kenya na baya-bayan nan, wasu kuma suna ba da shawarar yin zanga-zangar lumana.

Zanga-zanga: Abubuwan da Tinubu ya fadawa Malamai da Sarakuna a ganawarsa da su

Babu shakka akwai mutanen da su burinsu a yi zanga-zangar lumana ba tare da tashin hankali ba, amma yace damuwarsu ita ce a Nigeria ba a taba yin zanga-zanga ba tare da an sami matsala ba, Kuma tabbatar mun gano akwai yan kasashen waje da suke tunzura mutane su yi zanga-zangar ba tare da la’akari da illolin ta ba.nuna damuwa game da gaskiyarsu.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bukaci dukkan ‘yan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan kuma su yi tunani sosaiRundunar yan Sandan Nigeria ta gano masu shirya zanga-zanga irin ta Kenya a ƙasar  kafin su shiga wata zanga-zanga.”

Punch

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu Yanzu: Hukumar KNUPDA ta rushe gaban shagon jarumar Tiktok Rahama

Daga Rahama Umar Kwaru   Hukumar KNUPDA ta kaddamar da rushe...

Wata kungiya ta bukaci Gwamnan Kano ya dakatar da Shugaban karamar hukumar Gwale

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Wata kungiya mai zaman kanta mai...

Kwankwaso ba zai koma APC ba – Buba Galadima

Kusa a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya karyata jita-jitar...

Yadda gwamnan Kano ya ke rabon kujerun aikin hajjin bana kamar gyada

Daga Rahama Umar Kwaru Al'ummar jihar Kano na cigaba da...