Zanga-zanga: Abubuwan da Tinubu ya fadawa Malamai da Sarakuna a ganawarsa da su

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

A kokarin da Shugaba Bola Tinubu ya ke yi na ganin ya gamsar da yan Nigeria aniyarsa ta magance matsalolin kasar, a ranar alhamis ya gana da rukunonin shugabannin al’umma daban-daban daga cikin su akwai malamai da Sarakunan gargajiya.

Da yake yiwa malamai jawabi shugaba Tinubu ya ce duk wadanda su ke rura wutar sai yin zanga-zangar tsadar rayuwa a Nigeria, to ba masu kaunar kasar ba ne.

Ko da yake bai bayyana wani wanda ya dauki nauyin wannan zanga-zangar ba, amma ya ce wadanda ke fafutukar sai an yi zanga-zangar suna da fasfo na daban da idan al’amura sun dagule a Nigeria suna da kasar da zasu koma.

Talla
Talla

“Ba ma son mayar da Najeriya kamar Sudan. Muna maganar yunwa ne ba mutuwa ba. Dole ne mu yi hankali. Ya kamata mu yi taka tsantsan da jaririyar siyasar mu” . Inji Tinubu

” Suna ta tattauna yadda zasu gudanar da zanga-zangar a Internet, muna sane da su kuma muna kallon shirinsu na daukar nauyin zanga-zangar” Shugaban ya gaya wa malamai

Hasashen yanayin da zai kasance yau litinin a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria

Shugaba Tinubu ya bayar da hujjar cewa zanga-zangar an shirya ta ne cikin fushi da kiyayya, kuma idan ba a yi a hankali ba za ta iya rikidewa zuwa tashin hankali da mayar da kasar baya.

Ganawar shugaba Tinubu da Malaman Addinin Musulunci

“Masu daukar nauyin zanga-zangar ba sa kaunar kasarmu. Ba sa kaunar al’umma. Suna da shaidar zama a wasu kasashen,” inji Tinubu a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar.

Ya ci gaba da cewa shi ya dauki nauyin yakin neman zaben sa tun da farko, don haka bash da wani mutum ko kungiya da take juya shi ko ta fada masa yadda zai tafiyar da gwamnatinsa.

A nasa jawabin shugaban tawagar malaman Sheikh Bala Lau ya godewa shugaban kasar, Sannan ya yi alkawarin za su cigaba da yi masa addu’a da ba shi goyon baya da kuma wayar da akan al’umma.

” Zaman Lafiya shi ne komai a rayuwar al’umma, saboda zaman Lafiya da taimakon Allah Annabi Ibrahim ya fara roka a wajen Allah” a cewar Sheikh Bala Lau

Da yake ganawa da Sarakunan Gargajiya Shugaba Bola Tinubu ya fada masu cewa gwamnatinsa ta himmatu sosai wajen ganin ta magance matsalolin da kasar ta ke fuskanta.

” Babu shakka ni na nemi shugabancin kasar nan, lallai na zo gare ku don neman hadin kai da goyon bayanku, don haka ba ni da wani uzuri da zan nema, illa in tsaya na yi aiki tukuru don magance matsalolin da yan kasa su ke fuskanta”. A cewar Tinubu

” Na dauki duk wani laifi da gwamnatin da na gada ta yi, kawai abun da yake gabana shi ne yadda zan ciyar da Nigeria gaba “. Inji Tinubu

DSS Ta Ce Ta Gano Manufar Masu Son Yin Zanga-Zanga a Nigeria

Ya ce yana aiki ba dare ba rana domin ganin yan Nigeria sun sami jin dadi, yace shi yasa ya fara daukar matakai na matso da gwamnati kusan da al’umma, daga cikin su akwai batun baiwa kananan hukumomi yancin cin gashin kansu.

Ganawar Tinubu da Sarakunan gargajiya

” Na tura motoci dauke da Abinchi da takin zamani zuwa jihohin Nigeria, Sannan Ina kashe magudan kudade don ganin na inganta walwalar yan Nigeria”.

Ya ba su tabbacin nan ba da jimawa ba komai zai daidaita a Nigeria, saboda ya ce suna aiki tukuru domin warware matsalolin.

Talla

Da yake jawabi jagoran tawagar Sarakunan, Sarkin Muslim Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ce sun gamsu da bayanan da Tinubun ya yi musu kuma zasu cigaba da fada masa gaskiya kasancewar su kadai ne suke iya tunkararsa don su fada masa gaskiya.

” Mun gudanar da tattaunawa a tsakanin mu, kan matsalolin kasar da kuma fitar da shawarwan da zasu taimaka wajen magance kalubalen da yan kasar suke fuskanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...