Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce shi ma ya sha shiga zanga-zanga a lokacin mulkin soja “amma ba tare da tashin hankali ba”.
Shugaban na magana ne yayin da gwamnatinsa ke ta roƙon masu shirya zanga-zanga game da tsadar rayuwa da su ƙara mata lokaci don maganace matsalolinsu cikin ruwan sanyi.

“A lokacin mulkin soja, mun yi adawa da ‘yan kama-karya, kuma ina cikin mutanen da suka dinga zanga-zangar lumana ba tare da ƙone-ƙone ba,” a cewar shugaban lokacin da yake karɓar baƙuncin Jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills Jr. a yammacin yau.
DSS Ta Ce Ta Gano Manufar Masu Son Yin Zanga-Zanga a Nigeria
Ya ci gaba da cewa “mun yi bakin ƙoƙarinmu wajen tabbatuwar shekara 25 ta mulkin dimokuraɗiyya a jere kuma zan yi cigaba da rainon wannan dimokuraɗiyyar”, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ta bayyana.
Hukumar tsaron farin kaya ta ƙasar, DSS, ta yi gargaɗi dangane da shirin zanga-zangar tana mai cewa “burinsu shi ne kifar da gwamnati”.