Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Gobara ta yi sanadiyar hallaka yar Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Kano, Yusuf Kofar-Mata, tare da wasu yan uwansa guda biyu.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a shafin sa na Facebook a ranar Laraba.
Marigayiyar dai ‘yarsa ce mai suna Maimuna, sai yayarsa, Khadija, da matar dan uwansa, Juwairiyya.
Rahotanni sun bayyana cewa gobara ta kone gidan kwamishinan da ke Kofar-Mata a birnin Kano da safiyar Laraba yayin da iyalan ke barci.
Wata majiyar daga cikin danginsa ta ce gobarar ta lalata wasu kayayyaki masu daraja a gidan.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya soki gwamnatin Kano kan sabbin masarautu masu daraja ta biyu
Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Abdullahi Saminu, ya ce har ba a iya gano adadin barnar da gobarar ta yi ba, da kuma musabbabin tashin gobarar.
A halin da ake ciki, Kofar-Mata ya bayyana alhininsa game da rasuwar yar tasa da wasu ’yan uwansa guda.