Daga Rahama Umar Kwaru
Babbar Kotun Kano ta umarci sarakunan masarautun jihar da aka tube da su mayar mata da duk wani kaya mallakar gwamnati da ke hannunsu.
Kotun ta tabbatar da nadin Sarki Muhammadu Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 16, ta kuma haramta wa wadanda aka rusa masarautun nasu bayyana kansu a matsayin sarakuna.
Da take yanke hukuncin a ranar Alhamis, Mai sharia Amina Adamu Aliyu ta tabbatar da ikon da majalisar dokokin jihar Kano na yin dokoki.

Alkalin ta ci gaba da cewa don haka gyaran dokar masaraun jihar da majalisar ta yi yana kan ka’ida, haka ma hannun da Gwamna Abba Kabir ya yi a kan dokar wadda ta nada Sarki Muhammadu Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 16, bai saboda doka ba.
Kotun ta ce ta yanke wannan hukuncin ne bisa dogaro da sashi na 4,5,7, (a da b) sai kuma sashi na 101 a da a na kundin tsarin mulki Nigeria.
Dalilin da ya haifar da ruɗani a majalisar dokokin jihar kano akan Ganduje
Alƙalin ta kara da cewa abun da jami’an tsaro suka yi na dawo da sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero kuma suke gadin shi a gidan sarki na Nasarawa ya sabawa doka.
Sai dai kotun ta ki amincewa da rokon masu kara na cewa a fitar da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero daga Fadar Nassarawa.
Alkalin ta ce wannan ba hurumin kotun ba ne sai dai su kai wannan bukatar ga kotun tirabunal.