Kantomar Wudil ta biya wa dalibai 31 kuɗin makarantar koyon aikin jinya da Ungozoma

Date:

Daga Samira Hassan

 

Kantomar karamar hukumar wudil Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo ta ce ya zama wajibi ta inganta harkokin ilimi a yankin domin shi ne ginshikin cigaban kowacce al’umma.

” Na dauki nauyin biyawa waɗannan Matasa kuɗin makarantar koyon aikin jinya da Ungozoma ne domin kara yawan jami’an lafiya a wannan karamar hukumar, da kuma inganta lafiyar al’ummar mu a lungu da sako na wannan karamar hukuma ta Wudil”.

Hajiya Bilkisu Indabo ta bayyana hakan ne yayin bikin mika takardun shaidar samun guraban Karatu ga daliban a sakatariyar karamar hukumar wudil, ranar alhamis.

” Waɗannan matasa ‘ya’yan mu ne kannen mu ne, don haka ya zama wajibi mu taimaka musu don su sami ilimin yadda zasu kula da lafiyar al’umma da kuma rage yawan kalubalen da muke fuskanta a bangaren lafiya”.

Ta ja hankalin daliban da su mai da hankali wajen koyon abun da aka turasu, saboda da kudin al’ummar karamar hukumar wudil aka biya musu kudin makarantar.

Kotun Koli Ta Haramta Wa Gwamnoni Taba Kudaden Kananan Hukumomi

An dai raba daliban ne zuwa makarantun koyon aikin jinya ta Gwarzo da Danbatta da kuma Kano.

Da take jawabin game da yan jam’iyyar APC na karamar hukumar wudil da suka koma jam’iyyar NNPP, ta ce sun dawo NNPP ne bisa aiyukan alkhairi da gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin gwamnan Abba Kabir Yusuf take gudanarwa.

Rikicin Masarautun Kano: Yadda Matasa suka hana wakilin Sarki Sanusi shiga gidan sarkin Rano

” Sun kalli aiyukan gwamnan jihar Kano Abba Kabir da kuma irin aiyukan alkhairi da nake gudanarwa a wannan karamar hukumar, kuma Ina ba ku tabbacin zamu tafi da ku ba tare da nuna muku bambamcin ba”. Inji Bilkisu Indabo

Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo ta kuma bayyana irin aiyukan da ta gudanar a bangaren ilimi da lafiya da samar tsaro da tallafawa mata da Matasa don inganta rayuwar al’ummar karamar hukumar wudil.

Matasa Maza da Mata sama da dubu guda ne suka Sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar NNPP ta hannun kantomar riko ta karamar hukumar wudil.

 

Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar kano Alhaji Hashim Sulaiman Dungurawa shi ne ya jagoranci karbar sabbin masu sauya shekar, Inda ya ba su tabbacin jam’iyyar zata rungume su hannu bibiyu ba tare da nuna musu bambamci ba.

Ya kuma ce jam’iyyar NNPP ta na da kyawawan manufofi na ciyar da al’umma gaba, Inda yace hakan ce tasa yan jam’iyyar adawa suke ta barin jam’iyyunsu suna komawa jam’iyyar NNPP.

 

Ya kuma yabawa kantomar karamar hukumar wudil Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo bisa aiyukan alkhairin da taki gudanarwa , wanda yace koyi ta ke yi da jagoran jam’iyyar na kasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...