Rikicin Sarautar Kano: Kotu ta yi kwarya-kwaryar hukunci

Date:

 

 

Wata babbar kotun tarayya dake zaman ta a Kano ta yanke hukuncin cewa tana da hurumin sauraron ƙarar da aka shigar kan rikicin masarautar Kano, musamman kan abin da ya shafi kare hakkin ɗan’adam bisa dogaro da sashe na 46 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Alƙalin kotun, mai shari’a Liman Mohammed na babbar kotun tarayya da ke jihar, ya yanke hukuncin cewa sarkin kano na 15 Aminu Ado Bayero na da damar a saurare shi a kotu.

Tinubu ya mayar da martani game da faduwar da ya yi lokacin hawa mota

Sai dai alkalin ya ce ba magana ce a kan cancantar majalisar dokokin jihar na sauya dokar masarautun jihar ko kuma a’a ba.

 

Alƙalin ya bayyana cewa kotun ba ta ƙalubalantar damar da gwamnatin jihar ke da shi na naɗawa ko sauke sarki.

A ranar 23 ga watan Mayu ne gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun Kano ta 2024, bayan majalisa ta amince da ita.

Wannan ne ya bayar da damar komawar sarkin Kano na Muhammdu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16 tare da cire Aminu Ado Bayero daga kan mulki.

Sai dai jin kaɗan bayan haka ne Aminu Babba Danagundi ya shigar da ƙara yana ƙalubalantar sabuwar dokar, inda kotu ta bayar da umurnin tsayawa kan matsayin da ake.

Ranar Dimokaradiyya: Minista Abdullahi Gwarzo ya Bayyana Nasarorin Tinubu

Sai dai lamarin ya janyo ruɗani, inda Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II kowannensu ke iƙirarin shi ne halastaccen sarkin Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...