Daga Rahama Umar Kwaru
Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar kano ta ce ta haramta hawan sallar yayin bukukuwan Babbar Sallah a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanyawa hannu kuma aka turowa Kadaura24.
Sanarwar ta ce rundunar ta dauki wannan matakin ne sakamakon barazanar tsaro da za a iya samu idan an gudanar da hawan sallar.
Rikicin Sarautar Kano: Kotu ta yi kwarya-kwaryar hukunci
” Bayan ganawa da duk masu ruwa da tsaki a jihar kano, Rundunar yan sandan jihar kano ta hana yin duk wani hawa a yayin bikin sallah babbar dake tafe” a cewar Sanarwar
Ranar Dimokaradiyya: Minista Abdullahi Gwarzo ya Bayyana Nasarorin Tinubu
Rundunar ta ce ta haramta hawan a dukkanin fadin jihar kano baki daya.
Rundunar ta bukaci al’ummar jihar da su gudanar da sallar idin su cikin kwanciyar hankali da lumana a inda suke, su kuma cigaba da baiwa rundunar hadin kai don cigaba da inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.