Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Karamin ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya taya shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu murnar zagayowar ranar dimokuradiyya ta bana.
Abdullahi Tijjani Gwarzo, ya kuma taya ‘yan Nijeriya murna a matsayinsu na zaratan dimokuradiyya domin tunawa da zaben da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin 1993 da kuma samun dimokuradiyyar da ta shafe shekaru 25 ba tare da katsewa ba, ya kara da cewa, wannan babban mataki ne na ci gaban tsarin dimokuradiyya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga karamin ministan kan harkokin yada labarai Adamu Abdullahi ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.
Tsadar Rayuwa: Kar ku biye wa masu son yin zanga-zanga a Kano – Amb. Ibrahim Waiya
Ya bayyana cewa gwamnatin APC karkashin jagorancin shugaba Tinubu ta samu gagarumar nasara da ya kamata duk ‘yan Najeriya masu kishin kasa da masu son ci gaba su yi alfahari da su.
A cewarsa irin wadannan nasarorin sun hada da kaddamar da gina rukunin gidaje 3,112 a Karsana da Abuja, da kaddamar da ginin Renewed Hope Estate guda 250 a Katsina, Yobe, Gombe da Sokoto da kuma gina rukunin gida 500 na Renewed Hope a Kano da kuma rabon gidaje 8,925.
Ministan ya kara da cewa, shirin gina gidaje 100 a dukkan kananan hukumomin kasar nan 774 a karkashin asusun kula da marasa galihu na kasa, da kaddamar da aikin gina titin Legas zuwa Calabar a gabar teku da kuma gina babban titin Sokoto zuwa Badagry wani abin yabawa ne ga shugaban kasa.
Gwamnatin Kano ta tasamma warware rikicin ta da yan jaridun da sukai Mata tawaye
Sauran nasarorin da gwamnatin ta samu a cikin shekara guda da suka hada da inganta harkokin tsaro a kasar da irin jajircewa da matakan kishin kasa da aka dauka na gyara tattalin arzikin kasar.
Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su hada kai su yi aiki tukuru don gina kasa wadda al’ummarmu na gaba za su yi alfahari da ita. Abin da Shugaba Tinubu ke bukata daga dukkan ‘yan Nijeriya shi ne goyon baya da hadin kai don kai kasar nan zuwa ga tudun mun tsira.