Gwamnatin Kano ta tasamma warware rikicin ta da yan jaridun da sukai Mata tawaye

Date:

Daga  Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnatin jihar Kano da shugabannin kungiyar Wakilan kafafen yada labarai dake tura labaran kano sun yi wani taro a yammacin ranar Talata, inda suka tattauna batun da suka shafi dambarwar da ke tsakanin bangarorin biyu.

An gudanar da taron ne a cibiyar ‘yan jaridu ta NUJ, inda taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnatin kano da shugabannin kungiyar ‘yan jarida ta ‘Correspondent’ Chapel.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar yan jaridun Aminu Ahmad Garko ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.

Tawagar gwamnati karkashin jagorancin kwamishinan yada labarai Hon. Halilu Baba Dantiye, ya bayyana kudirin gwamnati na ganin an warware matsalolin da suke faruwa tsakanin su.

Za mu fara aikin da yan bori – hukumar tace Fina-Finai ta Kano

Ya ce gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta san muhimmancin ‘yan jaridu a cikin al’ummar da tsarin dimokuradiyya, ya kuma tabbatar wa ‘yan jarida a shirye suke su magance matsalolinsu.

Ya ce ya saurari korafe-korafen kungiyar kuma zai kaiwa gwamnan rahoton abun da ya faru da kuma shawarwarin yadda za a magance matsalolin.

A cewar Dantiye, gwamnan ya nuna damuwarsa kan faruwar lamarin inda ya umarce shi da ya gaggauta ganawa da ‘yan kungiyar domin a sasanta lamarin.

Wata Sabuwa: Sarki Aminu Ado Bayero ya baiwa hakiman Kano Sabon Umarni

“Wannan zai kai ga babban taro, wanda gwamnan da kan sa zai zauna da ku ya ji ta bakinku, sannan ya kuma dau matsaya.

“Na yi matukar farin ciki da yadda kuka karbe ni, hakika taron ya yi albarka kuma da yardar Allah za mu kai ga shawo kan matsalar .”

A jawabinsa shugaban kungiyar Wakilan kafafen yada labaran Aminu Ahmad Garko, ya yaba da wannan mataki na gwamnati tare da jaddada aniyarsu na yin aikin su bisa gaskiya da kwarewa.

Garko ya nuna farin cikinsa kan yadda gwamnatin jihar ke shirye-shiryen magance matsalolin da ke faruwa tsakanin ta da yan kungiyar .

“Har yanzu muna nan akan matsayar mu ta cewa ba za mu sake daukar rahoton dukkan al’amuran da suka shafi gwamnati ba, har sai an warware matsalolin .”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...