Daga Rukayya Abdullahi Maida
Guda cikin yan kishin kasa dake fafutukar gani yan Nigeria Sun sami saukin rayuwa, Alhaji Shitu Sani Marshall yace dimokaradiyya Koma baya ta kawo wa yan Nigeria ba ci gaba ba.
” Aiyukan raya kasa da cigaban jama’a da muka gani lokacin mulkin Sojoji ko rabinsun ba mu samu ba a cikin Shekaru 25 da mukai a tsarin mulkin Dimokaradiyya”.
Alhaji Shitu Sani Marshall ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da jaridar kadaura24 kan cikar Nigeria shekaru 25 a tsarin dimokaradiyya ba tare da katsewa ba.
EFCC ta fara bincike kan zargin da Ake yiwa Kwankwaso na almundahanar wasu kudade
Ya ce mulkin dimokaradiyya ban da koma baya da lalata tattalin arzikin kasa da gurbata tunanin mutane da cin hanci da rashawa babu abun da ya kawo wa dan Nigeria.
Ya ce idan ka kalli duk wasu manyan aiyukan raya kasa da ake alfahari da su a Nigeria zaka ga sojoji ne suka samar da su, kamar misalin asibitin malam Aminu kano dake jihar kano, da titin Kano zuwa Abuja da dai sauran su.
” Amma wannan tsarin na mulkin dimokaradiyya ba wani Abu da zaka iya nunawa a matsayin cigaban da ya kawowa yan kasa, Yan Siyasa sun lalata komai sun kasa samar wa yan kasa manyan muhimman kayan da suke da bukata, misali Wutar lantarki, lafiya, Abinchi da tsaro”. Inji Shitu Marshall
Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya Gana da Nuhu Ribado
“Kullum Kashe mutane Ake, kuma Allah ne kadai yasan yawan yan Nigeria da suke kwana da yunwa, wutar lantarki ta yi ƙaranci hakan yasa masana’antu sai rufewa suke yi rashin aikin yi kuma na kara ta’azzara, kuma duk waɗannan matsalolin yan siyasa ne suka jawo mana kuma suka kasa gyarawa”.
Shitu Sani Marshall ya ce wasu mutane sun kankane harkokin siyasar , shi yasa duk masu mutunci suka koma gefe suna kallo saboda an riga an lalata tsarin, an mayar da shi dole sai kana da kudi wanda kuma ba haka ya kamata tsarin ya zama ba.
Daga karshe Shitu Sani Marshall ya bukaci shugabannin kasar su mai da hankali wajen sauke nauyin dake kansu ko sa samar wa al’umma saukin rayuwa.