Daga Sani Idris Maiwaya
Ana sa ran Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II zai jagoranci Sallar Juma’a yau a masallacin Juma’a na fadar Sarkin.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Danburan Kano, a ranar Alhamis.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa tun bayan dawo da Malam Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano da kuma tsige Alhaji Aminu Ado Bayero tare da rusa masarautu guda biyar a ranar Alhamis din da ta gabata da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi, bayan sanya hannu kan sabuwar dokar masarautar Kano ta 2024, a can ake ta samun umarnin kotuna masu cin karo da juna.
EFCC ta fara bincike kan zargin da Ake yiwa Kwankwaso na almundahanar wasu kudade
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta bayar da umarnin dakatar da Aiwatar da sabuwar dokar data rusa Sarakunan kano, ya yin da wata babbar kotun jiha ta hana Alhaji Aminu Ado Bayero da gabatar da kan shi a matsayin Sarkin Kano da kuma korar shi daga gidan sarki na Nasarawa wanda ke kusa da gidan gwamnati.
Bayan haka, wata kotu ta dakatar da Malam Muhammadu Sanusi daga bayyana kansa a matsayin Sarkin Kano tare da ba da umarnin a fitar da shi daga fadar sarkin yayin da wata kotu ta dakatar da matakin.
Bayar da wadannan umarni na kotuna da ke cin karo da juna, alkalin alkalan Najeriya, Mai shari’a Kayode Ariwoola ya gayyaci shugaban babbar kotun tarayya da kuma babban alkalin Kano.
Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya Gana da Nuhu Ribado
Sanarwar da Danburan Kano ya fitar ta gayyaci jama’a da su zo su saurari hudubar da Malam Sanusi II zai gabatar.
Hakazalika, wata sanarwa da ta fito daga wani hadimin sarkin kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ita ma ta gayyaci jama’a da su fito domin raka sarkin zuwa masallacin juma’a na fadar sarkin don gudanar da sallar Juma’a.
An bayyana cewa sarki Aminu Ado Bayero zai fito domin tafiya masallacin fadar sarkin kano dake cikin gari ne da karfe 12:30 na rana.
Sai dai har yanzu hukumomin ‘yan sanda ba su ce uffan ba game da lamarin , wanda ake ganin ka iya haifar da tabarbarewar doka da oda.