Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Wata babbar kotun jihar Kano ta umurci sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero da ya daina bayyana kansa a matsayin sarki sannan kuma ta umurci kwamishinan ‘yan sanda na kano da ya fitar da shi daga gidan sarki na Nasarawa.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa kotun karkashin jagorancin mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta ba da umarnin a ranar Litinin, 27 ga Mayu, 2024.
Gaskiyar Lamari Kan Halin Da Ake Ciki a Masarautar Kano
Hakazalika, umarnin ya hana Alhaji Nasiru Ado Bayero, Dr. Ibrahim Abubakar II, Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa da Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya da su guji bayyana kansu a matsayin sarakunan Bichi, Gaya, Rano da Karaye.