Daga Mubina Mahmoud
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Hajiya Hauwa Isa Ibrahim a matsayin mai rikon mukamin Manajan Darakta ta gidan talabijin na Abubakar Rimi (ARTV).
Kadaura24 ta rawaito cewa nadin ya biyo bayan dakatarwar da aka yi wa manajan darakta Mustapha Indabawa.
Dakatarwar ta zo ne bayan jerin rahotannin da jaridar kadaura24 ta rika yi kan zarge-zarge da Ake yi masa, wanda hakan ya jawo hankalin hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta kano ta gudanar da bincike, inda daga karshe ta baiwa gwamnan Kano shawarar a dakatar da shi .
Gaskiyar Lamari Kan Halin Da Ake Ciki a Masarautar Kano
Wasikar nadin mai kwanan wata 27 ga Mayu 2024 ta samu sa hannun Abdullahi Baffa Bichi, sakataren gwamnatin jihar.
Wasikar ta umurce ta da ta karbi harkokin gidan talabijin din nan take.
Kafin nadin nata, Hajiya Hauwa Isa Ibrahim ita ce mataimakiyar Manajan Daraktan gidan talabijin din na ARTV.