Daga Nura Adam Lajawa
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce adadin mutanen da suka mutu a harin da wani matashi ya kai wa wasu masallata a wani masallaci a Kano ya kai mutum 11.
An yi zargin cewa matashin ya watsa fetur a masallacin tare da cinna wuta, sannan kuma ya kulle ƙofar masallacin, tare damutum kusan 40 a ciki.
Rahotonnin sun ce matashin ya kai harin ne sakamakon rigima kan rabon gado.
Hasashen yanayin da zai kasance yau alhamis a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria
Tuni dai ‘yan sanda suka ce sun kama maharin mai shekara 38.
Lamarin ya faru ranar Laraba lokacinj da mutane ke gabatar da sallar asuba a garin Larabar Abasawa da ke cikin yankin ƙaramar hukumar Gezawa a jihar.
‘Yan sanda sun ce wanda ake zargin ya shaida musu cewa ya aikata hakan ne da nufin ƙona wasu ‘yan uwansa da ke cikin masallacin waɗanda rigimar rabon gado ta shiga tsakaninsu.
Hukumar Hisbah ta sanya wa masu harkar DJ a Kano sharudda
“Abin da ya faru ba shi da alaƙa da ta’addanci, rigima ce da ta faru sakamakon rikicin rabon gado,” in ji Baturen ‘yan sandan yankin, Umar Sanda.