Hukumar Hisbah ta sanya wa masu harkar DJ a Kano sharudda

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta haramtawa maza su rika shiga wurin taron biki na Mata da sunan DJ a fadin jihar.

Babban kwamandan hukumar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana hakan a wani taro da yayi da wakilan kungiyar masu yin DJ a jihar Kano.

Ya ce matakin ya zama dole domin a hana cakuduwa tsakanin maza da mata a lokutan al’amuran biki.

Sheikh Daurawa ya bayyana cewa daga yanzu mata ne kawai za a bari su rika shiga wurin taron mata.

Hasashen yanayin da zai kasance yau alhamis a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria

Ya ce, “A matsayinmu na Musulmai, bai dace ba mu bari a rika cakuduwa maza da mata a wuri guda, saboda hakan ka iya haifar da fitina da kuma yadda badala.”

Ya kara da cewa a baya hukumar ta gana da masu Wuraren biki wato event center na jihar domin wayar da kan su game da dokokin da suka dace su rika kiyayewa kan abun da ya shafi ayyukansu.

A nasa jawabin, wakilin kungiyar masu yin DJ a Kano Ibrahim Abdullahi wanda aka fi sani da DJ Farawa ya yabawa hukumar bisa gayyatarsu da kuma ba su shawarwari kan sabbin tsare-tsare da hukumar ta bullo da su domin gudanar da harkokinsu.

Abduljabbar ya dakatar da lauyan dake kare shi a kotun daukaka kara ta Kano

Ya ce, “Mun yi farin ciki da gayyatar da hukumar Hisbah ta yiwa wannan kungiyar ta mu, Sun ba mu shawarar yadda yadda zamu kiyaye lokutan sallah a lokutan al’amura, da kuma wajibcin hana cakuduwar mata da maza a lokacin waxannan bukukuwa.”

Ibrahim ya ce duk DJn da ke gudanar da ayyukansa a jihar kano dole ne ya bi sabbin ka’idojin da hukumar ta fitar don gudun kada a sanya musu takunkumi.

Ya ce, “Wannan shi ne dalilin da ya sa muke kira ga dukkan masu harkar DJ a Kano da su yi rajista da ƙungiyarmu don gudun karya ƙa’idodin hukumar Hisbah.”

Ya kuma yi gargadin cewa, dum wanda yake DJ kuma yaki yin rijista da kungiyar mu to idan ya karya dokar Hisbah ba abun da zamu iya yi masa.

Biz point

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...