Mai Martaba sarkin na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai ziyara asibitin Murtala dake cikin birnin Kano domin duba marasa lafiya wadanda wani matasa ya bankawa wuta a masallaci a dai dai lokacin da suke gabatar da sallar asuba garin gadam dake Larabar Abasawa a karamar hukumar gezawa.
Alhaji Aminu Ado Bayero Bayan nuna jimami da alhinin abunda ya faru yayi addu’ar fatan samun lafiya a garesu da kiyayewar afkuwar hakan.
Sarkin yayi addu’ar Allah ya gafartawa wadanda suka rasu yasa aljanna madaukakiya itace makoma a garesu.
Hasashen yanayin da zai kasance yau alhamis a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun masarautar Kano Abubakar Balarabe kofar Na’isa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.
Adadin wadanda suka rasu cikin wadanda aka cinnawa wuta a masallaci a Kano na karuwa
A wani labarin kuma mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci kungiyoyin matan yan sandan kasar nan dasu kara himma wajen hada kan kungiyar matan yan sandan domin koyawa marayu da masu bukata ta musamman sana’oin dogaro da kansu.
Mai Martaba Sarkin ya bulaci hakan ne lokacin da kungiyar Matan yan sandan jihar kano Police Officers Wives Association suka kawo masa ziyara a fadar sa.
Alhaji Aminu Ado Bayero yace yaji dadin wannan ziyara da kungiya Matan yan sanda suka kawo masa tareda kudiurin da suke dashi na taimakawa marayu don su dogara da Kansu ba sai gwamnati ta basu aikin yi ba.
A nata jawabin Shugabar Kungiyar kuma Matar Kwamishinan Yan Sandan jihar Kano Hajiya Aisha Muhd Hussain Gumel tace tazo fadar Sarkin ne domin nuna goyon bayanta ga masarauta da kuma basu shawarwari domin cigaba kungiyarsu.