Iftila’i: Ana fargabar sama da mutane 30 sun kone suna tsaka da sallar asuba a wani masallaci a Kano

Date:

Daga Nura Adam Lajawa

 

Al’ummar garin larabar abasawa dake karamar hukumar Gezawa sun tashin cikin ruɗani bisa wayar gari da wani Iftila’i da yayi Sanadiyar konewar mutane sama da 30 a masallacin garin , inda ake zargin an saka musu wutar ne yayin da suke tsaka da sallar asuba.

Wani mazaunin garin ya shaidawa Kadaura24 cewa lamarin ya faru ne da asubahin wannan rana ta laraba, Inda yace ana wani ne ya kulle kofar masallacin bayan ya sanya musu wutar, Kuma har yanzu dai ba a san wanda yayi wannan aika-aika ba.

” Mafi yawan wadanda suke cikin masallacin sun jikkata, ba ma su kadai ba har da wadanda sukai Kokarin Kai musu dauki wutar ta lashi da yawa daga cikin su”. Acewar sa

Shi kuwa wani wanda ya tsallake rijiya da baya mai suna Yusuf Abdullahi yace yana cikin masallacin lokacin da lamarin ya faru yace suna tsaka da sallar asuba aka kunna wutar daga waje sannan aka cillota cikin masallacin.

Hasashen yanayin da zai kasance yau laraba a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria

” Allah ne kawai ya bani ikon fita Amma mutane da yawa ciki har da yan uwana guda biyu lamarin ya rutsa da su, kuma wutar ta yi musu illa babba saboda ko kasan mutum wallahi idan ka gan shi wallahi ba za ka iya gane shi ba”. Inji Yusuf Abdullahi

” Allah ne kadai yasan wanda ya Sako mana wutar amma tabbas wutar daga waje aka cillota cikin masallaci, kawai sai dai na ce Allah ya bayyana gaskiya.

Yace yanzu haka wadanda suka jikkatan suna bukatar gwamnatin jihar kano ta taimaka musu kuma ya yabawa al’ummar garin bisa yadda suka taimaka har jami’an lafiya suka je suka kwaso su zuwa asibiti.

Wakilinmu Wanda Ake gudanar da aikin Ceto rayukan masallatan ya shaida mana cewa tuni jami’an kula da lafiya suka je suka debo wadanda suka jikkatan Inda aka ajiye wasu a asibitin Sir Sunusi wasu kuma aka kai su asibitin Murtala da na Nasarawa duk a birnin Kano domin basu kulawar gaggawa.

Ministocin Gidaje Gwarzo da Dangiwa sun zama Gwarazan Ministocin Shekarar 2024

Sai dai Muna daf da kammala hada wannan rahotan muka sami labarin wani ya Kai kansu Ofishin yan sanda na garin inda ya ce shi ne ya sanya wutar a masallacin yayin da ake tsaka da sallar asuba.

Hakan tasa muka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa Wanda yace mu bashi lokacin domin gudanar da bincike kan lamarin. Idan ya hada binciken zamu sake tuntubarsa don sanar da al’umma halin da Ake ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...