Abduljabbar ya dakatar da lauyan dake kare shi a kotun daukaka kara ta Kano

Date:

Babbar kotun jjhar kano ɓangaren ɗaukaka ƙara ta ɗage sauraron ɗaukaka ƙarar da malam Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara ya yi a gabanta.

Gidan Radio Dala ya rawaito hakan ya biyo bayan wata takarda da Abduljabbar ɗin ya aikewa kotun wadda ya sanarwa da kotun cewar ya janye lauyansa daga cikin shari’ar.

Kotun ta ɗage shari’ar har zuwa lokacin da malamin zai gabatar da wani lauyan a gaban kotun.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Malam Abduljabra dai ya ɗaukaka karar ne akan hukuncin kisan da kotun shari’ar muslunci ta kofar kudu ta yanke masa a baya bisa samun sa da laifi.

Iftila’i: Ana fargabar sama da mutane 30 sun kone suna tsaka da sallar asuba a wani masallaci a Kano

Babbar kotun shari’ar Muslunci ta kofar kudu ta yankewa Abduljabbar hukunci kisa ta hanyar rataya sakamakon kama shi da laifin batanci, sai dai kasancewar malamin bai yadda da hukuncin ba hakan yasa ya ɗaukaka ƙararar.

Hasashen yanayin da zai kasance yau laraba a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria

Yayin zaman Kotun na yau Laraba 15-05-2024 karkashin jagorancin Mai Shari’a Nasir Saminu, an gabatar da takardar dakatar da lauyan wadda Malamin ya sanya wa hannu a ranar 10-05-2024.

Sai dai lauyoyin Gwamnati sun nemi kotu ta kori neman, da bukatar gyara a kan bayanan da Kotun baya ta yi amfani da su wajen yanke masa hukuncin kisa.

Sai dai kuma kotun ba ta karbi rokon lauyoyin Gwamnatin ba, kamar yadda wakilinmu na Kotu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...