Hasashen yanayin da zai kasance yau laraba a birnin Kano da wasu jihohin Nigeria

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Hasashen masana yanayi ya nuna cewa yau laraba 15-05-2024 dai-dai da 7 ga watan Dhul-Qada 1445 A.H , idan Allah ya so za’a sami zafin Rana a jihar Kano wanda zai kai 41 bisa ma’aunin zafi.

A jihar Kano dai babu yiwuwar samun ruwan Sama a yau.

Kadaura24 ta rawaito yanayi ranar zai kasance mai zafi sosai, Inda ranar zata fara zafi sosai daga misalin karfe 12 na rana har zuwa karfe 6 na yamma Sannan yanayin ya Sauya.

Hasashen dai ya nuna cewa ranar zata fara zafi ne daga lokaci da zafin ranar ya kai 39 inda zai sauya zuwa 41 bisa ma’aunin zafi.

Jihar Kano dai na fuskantar tsananin zafi a yan Kwanakin nan, Wanda hakan yasa masana suke baiwa al’umma mazauna jihar shawarar yadda zasu kare kan su daga illar da zafin ranar ka iya yi musu.

Gwamna Yusuf ya kaddamar da rabon tallafin ga mata duk wata a Kano

Shawarwarin da likitoci suke bayarwa sun hadar da takaita shiga Rana, yawaita shan ruwa, sanya kaya masara nauyi da dai sauransu.

Kaduna hasashen ya nuna a jihar Kaduna zafin rana zai kai 36 bisa ma’aunin zafi.

Abuja Kuna hasashen ya nuna zafin ranar zai kai 36 bisa ma’aunin zafi

Jihar Yobe kuma hasashen ya nuna cewa zafin rana zai kai 43 bisa ma’aunin zafi.

Jihar Kebbi ita kuwa zafin ranar zai kai 41 bisa ma’aunin zafi .

Yan sanda a Kano na bincike kan mutuwar jami’in kwastam da ake zargin ya kashe kansa

Birnin maiduguri na jihar Borno zafin ranar zai kai 43 bisa ma’aunin zafi.

Ku biyo mu gobe don kawo muku yadda hasashen zai kasance

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...