Rashin katabus: Gwamnatin Kano ta baiwa Pillars wa’adin wasanni uku na su farfaɗo da ƙoƙarin su

Date:

 

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da wa’adin wasanni uku ga mahukuntan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars domin dawo da ƙoƙarin ta da samun nasara a jere.

Mukaddashin Kwamishinan Matasa da Wasanni, Hamza Safiyanu Kachako ne ya ba da wa’adin, biyo bayan rashin kokari da kungiyar ke yi a kwanakin nan a gasar Firimiyar Najeriya ta kakar 2023/24.

Kano Pillars, wadda aka fi sani da “Sai Masu Gida,” ta fuskanci koma baya a wasanni na baya-bayan nan, inda ta sha kashi a hannun Bendel Insurance na Benin da ci 2-1. Kafin rashin nasarar kungiyar ta sha fama da rashin nasara a jere da suka hada da rashin nasara a hannun Shooting Stars da ci 1-2 da kuma rashin nasara da Enyimba International da ci 5-0.

Ya Kamata Gwamnati ta Fara Tilastawa Yan Kasuwa Don su Sauke Farashin Kayan su – Falakin Shinkafi

Sai dai Kwamishinan ya jaddada kudirin gwamnatin jihar, karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf na taimakawa Kano Pillars baya domin samun nasara.

Gwamnan Kano ya chanzawa wasu daga cikin Kwamishinonin sa ma’aikatu

Sai dai ya bayyana cewa dole ne a dauki kwararan matakai don dawo da kungiyar zuwa ga nasara, inda ya bayyana cewa gwamnati ba za ta sa ido kan yadda ƙungiyar ta Kano ke tabarbare wa ba.

Daga nan ne aka bukaci mahukunta da ma’aikatan kungiyar ta Kano Pillars da su sauya al’amura a wasanni uku masu muhimmanci da za su fara da wasan da za su kara da kungiyar Gombe United a ranar Lahadi, 21 ga Afrilu, 2024, a filin wasa na Sani Abacha, Kano.

Za a kuma ta buga wasa a waje da Akwa United da kuma karawar gida da Doma United ta Gombe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...