Daga Ibrahim Sani Gama
Shugaban gamayyar kungiyoyin kasuwar Singa dake jihar kano, Batista Junaidu Muhammad Zakari yayi kira ga Kamfanonin da suke Samar da kayayyakin masurufi, da su ji tsoron Allah wajen ragewa al’umma farashin kayayyakin sakamakon saukar da farashin Dala ke yi a kowacce rana.
Shugaban Gamayyar kungiyoyin ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi wakilin Kadaura24 a Kano.
Yace ya Kamata a ce kayan masarufi Sun Fara saukowa , Amma masu kamfanonin sun ki saukar da farashin nasu, Wanda hakan tasa al’umma suke zargin mune mukaki sauka da farashin kayan dukkuwa da karyewar farashin dala.
Batista Janaidu zakari,ya bayyana cewa, Kungiyar a shirye take a kodayaushe wajen ci gaba da marawa Gwamnatin jihar Kano baya domin inganta jin dadi da walwalar jama’ar jihar Kano.
Ya Kamata Gwamnati ta Fara Tilastawa Yan Kasuwa Don su Sauke Farashin Kayan su – Falakin Shinkafi
Ya bukaci kungiyoyin da sauran al’ ummar Kasuwar ta Singa da su kasance masu baiwa Kwamatin tsaftar Muhallin da Ma’aikatan da za su yi aikin cikakken hadin domin ciyar da kasuwar da Kasuwanci gaba a fadin kasar nan.
A Wani labarin kuma Shugabancin Gamayyar Kungiyoyin yankasuwar Kwanar Singa ya jaddada Kudirinsa na kara tsaftace Kasuwar yadda Ya kamata.
Shugaban Sashen kula da harkokin Sharia kuma Shugaban Kwamatin tsaftar Muhalli Batista Abdullahi Usman Ganaru ne ya bayyana haka a lokacin Kaddamar da fara aikin tsaftar Kasuwar ta Singa.
Abdullahi Ganaru yace,Kungiyar ta bijiro da tsaftar Muhallin ne,domin marawa yunkurin Gwamatin jihar Kano baya na ganin ta tsaftace lunguna da sako na birnin Kano da kewaye.
Kotu Ta Jingine Dakatarwar Da Aka Yi Wa Ganduje
Shugaban Kwamatin ya bayyana cewa, Kungiyar ta ware Makudan Kudade domin aiwatar da aikin tsaftar Kasuwar ta Singa da kuma, Sauran Al’amuran da za su kawowa yankasuwa da Alummar jihar Kano ci gaba.
Haka Zalika,Shugaban Kwamatin yace,Kwamatin ba zai saurarawa duk wani da aka samu da laifin yin kashi ko fitsari ba a guraren da basu Kamata ba,inda yace yin fitsari ko kashi zai haifar da Barazana ga lafiya ga dukiyoyin Alumma.
Ya kuma kara da cewa,Kungiyar ta hada kai da Ma’aikatar Muhalli da kula da sauyin yanayi ta jihar Kano da Kwararru da suke da sani a bangaren tsaftar Muhalli da kula da lafiyar Al’umma domin cimma Nasarar shirin.