Tsohon dan kararar mataimakin gwamna a jam’iyyar APC a Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo na yiwa daukacin al’ummar musulmi barka da sallah.
Kadaura24 ta rawaito a wani sakon taya murna Alhaji Murtala Sule Garo ya ce bikin Sallar bai takaita ba ne kawai ga kammala azumin wajibi na watan ramalana, ya hada da fadakar da tunatard al’umma don ganin an samu zaman lafiya da arziki mai daurewa a JIhar Kano da Kasa baki daya.
Yanzu-yanzu: CBN Ya Sake Karya Farashin Dala a Nigeria
Sule Garo ya ce, “Ina taya daukacin al’ummar musulmi musamman na jihar Kano barka da sallah.
“Muna godiya ga Allah madaukakin sarki da ya bamu ikon azumtar watan ramalana. Allah ya karbi ibadinmu, ya yafe mana kurakuranmu, ya kuma kara aramana lokaci nan gaba.
“Ina kira ga al’umma musulmi da su yi amfani da darusan da muka koya cikin wannan wata mai alfarma dan tabbatar da zama lafiya da kaunar juna a jiharmu da kuma kasa baki daya.
Tabbas ‘yan najeriya na cikin wani mawuyacin hali sakamakon tabarbare tattalin arziki. Amma duk da haka ba ma cire kauna ga kasarmu ba. Dan haka wannan lokaci wata dama ce a garemu da za mu ci gaba da addu’o’i Allah ya kawo mana mafita da arziki mai daurewa.”
Barka da Sallah