Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
An haifi Saratu Gidado wadda akafi sani da Daso a ranar 17 ga watan janairu na shekara ta 1968 a jihar Gombe dake arewa maso gabshin Nigeria.
Saratu Gidado ta yi karatunta na firamare a chiranchi dake karamar hukumar Gawle a jihar kano ta kano, kuma ta shiga masana’antar kannywood a s shekara ta 2000.
ta bayar da gudunmwa a fina-finai da dama da daga cikin su akwai: Linzami da wuta, Mashi, Fil’azal, Jaridar, Garwashi, Mu rike amana,, Sakace, Takun saka, Sammatsi, Bakar tukunya, Gabas, Lamba, Yayan baiwa, Sabon shafi da dai sauransu.
Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa Jarumar kannywood Daso Rasuwa
Hajiya Saratu Gidado tana daga cikin Jakadun Sarkin Kano tun lokacin sarkin Kano na 14 Muhammadu Sanusi II har zuwa Sarkin kano na yanzu Alhaji Aminu Ado Bayero.

Ka Yi Aikin Dake Gabanka Ka Rabu Da Ganduje – Kwankwaso Ya Fadawa Abba Gida-gida
Marigayiyar ta kuma shahara wajen nemawa marasa karfi da Marayu taimako musamman a shafukan sada zumunta.
Hajiya saratu Gidado wadda ta Shahara a masana’antar Kannywood ta rasu ne ba tare da wata rashin lafiya ba kamar yadda Shugaban kungiyar jaruman Kannywood Alhsan kwalli ya Shidawa manema labarai.
Tuni dai an yi jana’izar ta kamar yadda Addinin Musulunci yayi tanadi, kuma mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ne ya jagoranci jana’izar ta ta a fadar sarkin dake kofar kudu.