Daga Umar Sani Kofar Na’isa
Gidauniyar IGE BABA DIGGI karkashin jagorancin shugaba Alhaji Umar Namashaya Diggi ta rabawa al’ummar karamar hukumar Kalgo Tallafin kudi Naira dubu goma goma ga mutane dari shida a garin Diggi.
Shugaban kwamitin rabon tallafin kudin Alh Altine Dandiggi yace manufar shirin zakulo mutane 600 domin a basu kudi hannu don rage musu radadin a wannan wata mai alfarma.
Ku Fara Neman Watan Shawwal A Gobe Litinin – Sarkin Musulmi Ga Musulmin Nigeria
A jawabin wakilin kantoman karamar hukumar mulki ta kalgo Alh Alu Diggi da wakilin ubankasar Diggi Alh Yusuf Aliyu sun yabawa gidauniyar bisa wannan aikin alheri don haka suka yi kira ga masu hannu da shuni suyi koyi da wannan abin alheri.
Ramadan: Abubuwan da ya kamata ku sani game da Khatamar Al-Qur’ani ta bana a masallacin Harami
A nasa jawabin Shugaban gidauniyar Alh Umar namashaya diggi yayi alkawarin cigaba da wannan rabon tallafin kudin lokaci bayan lokaci domin jin kan alummar karamar hukumar Kalgo.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun godewa gidauniyar bisa wannan tallafin kudi da aka basu.