Daga Rahama Umar Kwaru
Farashin kankara a birnin Kano ya ruguzo daga Naira 700 zuwa 150 sakamakon yanayinhazo da sanyin da mazauna garin suka fara fuskanta tun ranar Lahadin da ta gabata.
A makon da ya gabata ne aka siyar da kankarar da ake yainta a farar leda ta Santana” wadda ake cewa bugun gardi a tsakanin Naira 600 zuwa N700 yayin da aka siyar da kankarar “pure water” akan Naira 200 zuwa 300 sakamakon yawaitar masu bukatar su saboda tsananin zafin da aka yi da kuma karancin wutar lantar a birnin.
Bidiyon Dala: Kotu ta Yanke Hukunci Kan Karar da Ganduje Ya Kai Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Kano
Wani bincike da aka gudanar ya jiya alhamis a wasu wurare a cikin birnin ya nuna cewa farashin kankarar ya ragu matuka kuma an sayar da kankarar “pure water a tsakanin Naira 50 zuwa 100 yayin da kankarar bugun gardi yanzu ake sayar da ita tsakanin N150 zuwa N250.
A bayan dai kankarar ta sami karbuwa ne a wajen mutane saboda tsananin zafin Rana da Aka yi da kuma karancin wutar lantar da aka fuskanta , a yan Shekarun nan dai akan gudanar da ibadar azumin watan Ramadana ne a watan Maris ko Afrilu lokacin da yanayin zafe ke kaiwa salshiyos 40 ko kuma fi.
Yanzu-yanzu: Sarki Musulunci ta tabbatar da Gani watan Azumin Ramadana
Wata mai sayar da kankara a kan titin Katsina, Halima Aliyu, wadda ta fara sana’ar a shekara ta hudu, ta ce ta sayi ledar kankara ta pure water a kan kudi Naira 1,000 (N50 kan kowacce leda) kuma tana sayar da ita kan Naira 2,000 a halin yanzu.
A cewar ta, a cikin makon da ya gabata ta sayar da kankarar pure water a kan kudi Naira 250 kowacce leda daya wanda jakar ledar ta kai kusan N5000.
Cin Hanci: Yan Sanda Sun Gurfanar da Jarumar Kannywood, Amal, a Gaban Kotu
Ta ce a makon da ya gabata lokacin da yanayi ya yi zafi, ta sayar da kankara bugun gardi a kan kudi Naira 700, amma yanzu farashin ya fadi saboda yanayi da karancin masu bukata.
Umar Hamza, wanda ke gudanar da shagunan sanyin kankara a Asada Small Scale Enterprise, ya koka da karancin masu sayan kankarar a sakamakon a yayin sauyin yanayi.
Ya ce, “A kullum a makon da ya gabata ya kan sayar da jakar ledar pure water guda 300, amma yanzu ko rabi bama iya sayarwa. Haka ita ma bugun gardi.