Da Safiyar yau Alhamis ne Ƙungiyar masu ƙananan Masana’antu ta Najeriya (NASSI) da Kamfanin Glodanif Energy Limited, suka sanya hannu akan yarjejeniyar samarwa da Ƙananan Masana’antu wutar solar mai ƙarfin Megawatts 3 wadda aka yiwa take da (Green Industrialisation Iniative), a Jahohin Najeriya 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ƙungiyar masu ƙananan Masana’antun ta ɗauki wannan mataki ne a ƙoƙarin da take yi wajen magance wa dukkan masu ƙananan Masana’antun matsalar da suke fuskanta a fannin wuta, wadda ta kasance ƙashin bayan aikin nasu.
Tinubu ya Haramtawa Ministoci da sauransu tafiye-tafiye zuwa kasashen waje
Shugaban Ƙungiyar masu ƙananan Masana’antun ta Najeriya Chief Dakta Solomon Daniel Bompa ya ce, manufar shirin shine domin wadata ƙananan Masana’antun ƙasar da wutar da zasu ke amfani da ita wajen yin ayyukan su na yau da kullum.
Harma ya ce tuni an zaɓi jihohin Osun, Oyo da kuma Gombe domin fara aikin wutar solar ta yadda zai zama an aiwatar da aikin, domin dukkan ƙananan Masana’antu su ci gajiyar shirin.
Dalilin Da Yasa ’Yan Sanda Suka Nemi Murja Kunya Ta Biya Su Diyyar Naira Dubu 500
A nasa ɓangaren Ma’ajin ƙungiyar masu ƙananan Masana’antun ta Najeriya Dakta Abubakar Tanko Bala ya ce, waɗanda zasu amfana da wutar sune masu ƙananan Masana’antun dake ƙarƙashin ƙungiyar dake faɗin Ƙasar.
Abubakar ya ƙara da cewa, sun samar da shirin ne ta yadda zai zama an rage wa masu ƙananan Masana’antu wahalhalun da suke fuskanta musamman ta fuskar koma baya dama durƙushewar kamfanonin da ake fama da su a faɗin Ƙasar saboda rashin tsayayyiyar wutar lantarki.
An Baiwa Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Mukami a Darikar Tijjaniyya
Dakta Tanko Bala ya kuma ci-gaba da cewa, abin sha’awar shine yadda wutar da zasu samar, ta kasance mai inganci fiye da wadda suke amfani da ita halin yanzu, baya ga sauƙin da zasu samu wajen kashe kuɗi dama sauran wahalhalu da ake yiwa wutar.
Taron sanya hannu akan yarjejeniyar dai ya gudana ne a shalkwatar ƙungiyar dake babban birnin tarayya Abuja, inda ya sami halartar dukkan masu ruwa da tsakin ƙungiyar, dama na kamfanin Glodanif Energy Limited da dai sauransu.