Tinubu ya Haramtawa Ministoci da sauransu tafiye-tafiye zuwa kasashen waje

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

 

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya haramta wa ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati yin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje a aljihun gwamnati.

Haramcin wanda zai dauki tsawon watanni uku a matakin farko zai fara aiki a ranar 1 ga watan Afrilu, 2024.

Haramcin ya zo ne cikin wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Hon. Femi Gbajabiamila da sakataren gwamnatin tarayya George Akume wadda aka sanya wa hannu a ranar 12 ga watan Maris din 2024.

Dalilin Da Yasa ’Yan Sanda Suka Nemi Murja Kunya Ta Biya Su Diyyar Naira Dubu 500

Wasikar haramcin ta kara da cewa, “Shugaban kasa ya damu da almabazzarancin da ke kunshe da tafiye-tafiyen jami’ai da sauran hukumomin gwamnati, da kuma bukatar da ke akwai ta mambobin majalisar ministoci da shugabannin MDA na su mai da hankali kan ayyukansu na cikin gida maimakon balaguro”

Wasikar ta ce “Bisa la’akari da kalubalen tattalin arziki da ake fuskanta a halin yanzu da kuma bukatar gudanar da harkokin kasafin kudi, na rubuto ne domin in isar da umarnin shugaban kasa na sanya dokar hana fita na wucin gadi ga dukkan jami’an gwamnatin tarayya a dukkan matakai har na tsawon watanni uku daga Afrilu 2024.”

Wani mutum ya makance bayan amfani da fitsari don maganin ciwon ido

Tinubu ya kara da cewa, daga yanzu jami’an gwamnati da ke da niyyar tafiya duk wata ziyarar aiki a kasashen waje dole ne su nemi amincewar shugaban kasa a kalla makonni biyu kafin su fara shirin tafiyar, kuma fadar shugaban za ta amince ne da tafiyar kawai idan ta zama dole.

Idan ba a manta ba, a watan Janairu ne shugaba Tinubu ya ba da umarnin rage yawan tawagar masu yi masa rakiya da na mataimakinsa a tafiye-tafiyen cikin gida zuwa 25 da kasashen waje zuwa mutum 20 kacal.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...