An Baiwa Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Mukami a Darikar Tijjaniyya

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Guda cikin jikokin Shehu Ahmadu Tijjani dake kasar marocco Sheikh Uzair ya baiwa sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero mukamin mukaddami a cikin darikar Tijjaniyya.

Idan za’a iya tunawa sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai kasar marocco bisa gayyatar masarautar Kasar, inda ya halacci taron lacca kan azumin watan Ramadana ake gudanarwa duk shekara a Kasar.

Wannan ita ce takardar nadin

Bayan kammala taron ne guda cikin jikokin Shehu Ahmadu Tijjaniyya mai suna Sheikh Yahuza ya mika takardar mai dauke da sa hannun sa , inda aka bashi mukaddami a cikin darikar ta Tijjaniyya.

Dalilin Da Yasa ’Yan Sanda Suka Nemi Murja Kunya Ta Biya Su Diyyar Naira Dubu 500

A Wani video da makusantan sarkin Kano suka Rika sanyawa a Facebook ya nuna yadda guda cikin yan tawagar sarkin ya fassara mukamin da aka baiwa sarkin a daidai lokacin da ake mikawa sarkin Kano takardar tabbatar da nadin nashi.

Tinubu ya Haramtawa Ministoci da sauransu tafiye-tafiye zuwa kasashen waje

” Kamar yadda kuke gani maulana Sheikh Uzair yana baiwa mai martaba Sarki ijaza ta darikar Tijjaniyya, wacce take amma mudlaka daga kansa zuwa kakansa maulana shehu Ahmadu Tijjani RTA, saboda haka mai martaba Sarki yana daga cikin manyan mukaddamai na darikar Tijjaniyya wajen bada darika da kuma kaddamar da mukaddamai a koda yaushe”.

Wannan mukami dai zai baiwa sarkin damar shiga a dama da shi cikin al’amuran da suka shafi darikar Tijjaniyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...