Matar Shugaba Tinubu ta bayyana dalilin da suka sa bata tsoron mutuwa

Date:

Mai dakin Shugaban Kasa Bola Tinubu ta ce yanzu haka shekarunta na haihuwa sun kai 60, don haka ta yi tsufan da ba ta tsoron mutuwa.

Remi Tinubu ta bayyana hakan ne a Fadar Sarkin Bauchi, Dokta Rilwani Suleiman Adamu ranar Talata, kan wani bidiyon barazanar kisa da wani malami Sunusi Abubakar ya yi mata a kwanakin baya.

Remi ta kai ziyara jihar ne domin kaddamar da aikin makaranta da cibiyar horaswa kan fasahar bayanai da gwamnati ta yi a jihar.

Ramadan: Zamu Kashe Naira Miliyan 15 Wajen Ciyar da Masu Karamin Karfi -Kantoman Dawakin Tofa

A kwanakin baya ne dai bidiyon ya karade soshiyal midiya, inda malamin ya ce ya kamata a kawar da ita daga doron kasa, kafin daga bisani ya janye kalamansa bayan shan suka daga mutane.

“Ina son mika godiya ga Gwamna saboda tabbatar da rayuwata bata cikin hadari. Amma abin da zan ce shi ne na yi tsufan da bana tsoron mutuwa.

Yanzu-yanzu: Tinubu Ya Sa a Buɗe Iyakokin Najeriya Da Nijar

“Yanzu haka shekaruna 60, ba na jin ya kamata a ce ma na ji tsoronta. Duk da haka na gode Allah da na samu kwarin guiwar zuwa duk da waccan barazanar.

“Najeriya ta mu ce gaba daya, ya dace mu hada kai a yanzu fiye da a baya,” in ji Remi Tinubu.

Tun da fari dai Gwamnan Jihar Bala Muhammad ya nemi afuwar mai dakin shugaban a madadin ilahirin al’ummar jihar bisa waccan barazanar da aka yi mata a baya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Magance sheye-shaye ne kadai zai kawo karshen matsalar tsaro da talauci a Nugeria – Shugabar LESPADA

Daga Usman Usman   Ambassador Maryam Hassan shugabar kungiyar wayar da...

‎Kungiyar APC Patriotic Volunteers Ta Mayar Da Martani Kan Sauke Alhaji Usman Daga Mukamin Wazirin Gaya

Daga Isa Ahmad Getso ‎ ‎Kungiyar APC Patriotic Volunteers ta bayyana...

Rahoto: An kwantar da Buhari a ICU a Landan

  Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na fama da rashin...

Kacibus: A karon farko an hadu tsakanin Gwamnan Abba da Sarki Aminu Ado a Madina

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   A karon farko an hadu tsakanin...