Daga Rabi’atu Yunusa Adam
Kwamandan Hukumar Hisbah ta jihar kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya mika godiya ga wasu muhimman mutane da yake sun taka rawa wajen sulhunta su da gwamnan Kano bisa abun da ya faru a tsakanin su.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Malam Aminu Daurawa ya ajiye mukamin sa ne bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya kalubalanta yadda hukumar take gudanar da aikin kamo mata masu aikata bidala a jihar.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana haka ne Lokacin da ya ke komawa Ofishinsa Na Shugaban hukumar Hisba a ranar Talata.
Gwamnan Kano ya Turawa Majalisar Dokoki Sunayen Kantomomi 44 Domin Tantancewa
“Ina godiya da mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III wanda da kansa ya kirawo ta waya akan batun, sai Alhaji Dahiru Mangal Wanda shi kuma har zazzabi ma yayi saboda abun da ya faru, shi kuwa Farfesa Ibrahim Maqari Babban Limamin masallacin kasa tun daga Abuja ta taso ya zo Kano saboda abun da ya faru “.
Bidiyon Dala: Kotu ta Yanke Hukunci Kan Karar da Ganduje Ya Kai Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Kano
Malam Daurawa ya kara da cewa dole ya godewa Sheikh Ali Isa Fantami Wanda shi kuma Kwankwaso ya Samu ya yiwa magana akan batun, shi kuma Kwankwaso matsayinsa na jagora ya kirawo ni a waya muka tattauna akan batun. Don haka dole Ina godewa wadannan mutane da ma wadanda ban sami damar ambatar sunansu ba, musamman Inuwar hadin kan malaman jihar kano da sauran su.
Sheikh Daurawa ya kuma bayyana shirin hukumar ta Hisba na ci gaba da gudanar da ayyukansu domin tsaftace ayyukan badala a jihar Kano.