Daga Halima Musa Sabaru
Gwamna Abba Kabir-Yusuf na jihar Kano ya mika sunayen shugabannin riko na kananan hukumomin jihar ga majalisar dokokin jihar ta domin tantance su.
Wannan na zuwa ne makonni uku, bayan karewar wa’adin zababbun shugabannin kananan hukumomin jihar.
Kakakin majalisar, Ismail Falgore, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a zauren majalisar yayin da yake karanta takardar bukatar da gwamnan ya turawa majalisar.
Gwamna Abba Kabir Ya Mikawa Majalisar Kano Sunayen Kwamishinonin Da Zai Nada
Yayin da yake gabatar da sakon, shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini (NNPP-Dala), ya ce bukatar gwamnan ta biyo bayan karewar wa’adin zababbun shugabannin kananan hukumomin da mataimakansu ne tun a ranar 12 ga watan Fabrairu, 2023.
A cewarsa, jerin sunayen sun kunshi shugaba da mataimakinsa da sakatare na kowace karamar hukuma cikin kananan hukumomi 44 da ake da su a jihar.
Bidiyon Dala: Kotu ta Yanke Hukunci Kan Karar da Ganduje Ya Kai Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Kano
Shugaban masu rinjaye ya bayyana cewa sashe na 58 na dokar kananan hukumomi ya bayyana cewa, idan wa’adin shugabancin kananan hukumomin jihar ya kare ya zama wajibi a gudanar da zabe.
Dokar ta kuma bayyana cewa gwamna na iya nada shuwagabannin riko da za su rika kula da harkokin majalisun kananan hukumomin na tsawon watanni uku.
Bayan tattaunawa, majalisar ta amince da kudurin, tare da kafa kwamitin wucin gadi da zai tantance wadanda aka nada a ranar Laraba 6 ga watan Maris.