Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta yanke shawarar dage wasu takunkumin da ta kakabawa jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Guinea.
An dauki wannan kuduri ne a wani babban taro na musamman kan harkokin zaman lafiya, siyasa da tsaro a yankin ECOWAS da aka gudanar a Abuja ranar Asabar.
Tinubu Ya Bayyana Hanyoyin Da Za’a Daidata Tsakanin ECOWAS Da Nijar Burkina Faso da Mali
Kungiyar ta ECOWAS cewa ta zata dage takunkuman siyasa da aka kakabawa Jamhuriyar Nijar ba, Inda suka ce an dage sauran takunkuman da suka hadar da na tattalin arziki da sauran, sannan kuma ta dage wasu takunkuman kudi da na tattalin arziki da ta kakabawa Guinea da wasu takunkuman da aka kakabawa Mali.