Hanyoyi takwas da ake ku bi don sayen shinkafar kwastam mai araha

Date:

Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya kwastom ta fara sayar da shinkafa kan farashin mai sauki ‘yan kasa.

Matakin na daga cikin ayyukan rage radadin tattalin arzikin da ‘yan NAjeriya ke fuskanta

Mai magana da yawun hukumar Abdullahi Maiwada ya shaida wa BBC cewa shinkafar da hukumar ke sayarwa, shinkafa ce da jami’an hukumar suka kama a lokacin da aka shigar da ita kasar ba bisa ka’ida ba.

Ya ce hukumar ta kai shinkafar kotu inda suka samu sahalewar kotu domin sayar da ita ga talakawan kasar.

Kamata yayi Gwamnati ta cirewa kayan masarufi haraji ta mai dashi kan Giya, sigari da kayan kyalekyale – Falakin Shinkafi

Abdullahi Maiwada ya ce an fara sayar da sayar da shinfara ne a jiya Juma’a a jihar Legas, a matsayin gwaji kafin daga baya hukumar ta fadada aikin zuwa sauran jihohin kasar da take da irin wadannan kaya da ta kama.

Kakakin hukumar ya ce suna sayar da buhu mai nauyin kilogiram 25 na shinkafar a kan kudi naira 10,000.

Matakan da hukumar ke bi wajen sayar da shinkafar

Abdullahi Maiwada ya ce hukumar na bin wasu matakai na tantancewa kafin ta sayar da shinkafar ga al’umma kamar haka.

1. Amfani da NIN – Ya ce hukumar na amfani da lambar da ke jikin katin dan kasa ta NIN wajen tantance mutanen da take sayar wa shinkafar, don haka dole sai wanda ke da lambar NIN zai samu damar sayenta.

Kotun ta Yanke Hukunci Kan Kalubalantar Hukuncin Kashe Sheikh Abduljabbar

2. Mutanen da ke kusa da inda hukumar ta kama kaya- Abdullahi Maiwada ya ce hukumar na sayar da shinkafar ne kawai ga mutanen da ke kusa da inda ta kama shinkafar, ”don haka duk mutumin da ya zo daga nesa ba zai samu sayen shinkfara ba”, in ji shi.

3. Masu sana’ar hannu – Kakakin hukumar Kwastam din ya ce daga cikin rukunin mutanen da hukumar ke sayar wa shinkafar su ne masu sana’ar hannu. Ya ce an yi hakan ne domin tallafa musu wajen bunkasa sana’o’insu.

4. Malaman makaranta – Hukumar ta ce malaman makaranta na daga cikin rukunin mutanen da za su amfana da sayen da sayen shinkafar da hukumar kwastam ke sayarwa.

5. Masu sharar titi – Abdullahi Maiwada ya kara da cewa su ma mutanen da ke sharar titi na daga cikin rukunin mutanen da hukumar ba domin sayar musu da shinkafar.

6. Mutanen da suka fi tsananin bukata – Kakakin hukumar ya shaida wa BBC cewa dama makasudin sayar da shinkafar shi ne rage wa al’immar radadin tsadar rayuwa da ‘;yan kasar ke fuskanta, don haka ya ce suka fi bayar da fifiko kan mutanen da ke cikin tsananin bukata.

7. Mata – Wasu rukunin mutanen da za su amfana da shinkafar kwastam din mai cike da rahusa su ne mata, musamman marasa karfi, wadanda ke rike da kananan yara.

8. Kungiyoyin addini – Kungiyoyin addini na daga cikin al’umomin da za su amfana da wannan sayar da shinkafa da hukumar kwastam ke yi, kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook.

Hukumar ta kuma gargadi ‘yan kasar da ke da aniyar sayar da shinkafar ga ‘yan kasuwa, da su guji yin hakan.

Abdullahi Maiwada ya ce duk wanda ya yi haka zai fuskanci fushin hukumar, sannan kuma ya ce hukumar za rika sanya idanu a kasuwanni domin ganin ko ‘yan kasuwa za su sayi shinkafar domin sayarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...