Daga Rahama Umar Kwaru
Babbar kotu jihar Kano karkashin mai sharia Sunusi Ado Ma’aji tayi watsi da karar da daliban malam Abduljabbar kabara suka shigar suna neman a basu dama don daukaka kara kan hukuncin kisa da kotun Shari’ar musulinci dake kofar kudu tayi wa malam Abduljabbar din tin a shakarar data gabata.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito wata kungiyar daliban malam Abduljabbar daga jihar Bauchi, karkashin jagorancin Musa Sani Turaki Fali ne ya nemi kotun ta bashi damar daukaka kara, kan hukuncin da kotun Shari’ar Musulunci dake zamanta a Kofar kudu ta yanke.
Kotun dai kar kashin jagoranci mai shari’a Abdullahi Sarki Yola ta ce ta sami Abduljabbar da laifin yin kalaman da basu dace ba akan manzon Allah sallallahu alaihi wasallam, a saboda haka ne kotun ta ce ta yanke masa hukuncin kisa.
Majalisar Dattawa ta Bayyana Dalilanta na Bincikar Gwamnatin Buhari
Toh sai dai Kotun ta ce ta kori ƙarar ne a sakamakon gaza gabatar mata da gamsassun hujjoji da ɓangaren masu ƙara suka yi, wanda zai sanya ta sahale musu su ɗaukaka ƙarar a madadin Malamin.
Dama dai a ƙaidar doka, waɗanda suke da damar ɗaukaka ƙara akan shari’ar sune, Malamin da kansa, Ɗansa Ko kuma mahaifin sa.
Babu Isassun Kayan Aikin da Za’a Aiwatar da Ilimi kyauta kuma Dole a Kano – Kungiyar Plane
Abin Jira a gani shi ne ko masu ƙarar zasu rungumi ƙaddara su karɓi Hukuncin ko kuma zasu ɗaukaka ƙara.
Wata Kotun shari’ar Musulunci dake zamanta a ƙofar kudun Kwaryar Birnin Kano ce dai, ta yanke wa Shehin Malamin Hukuncin Kisa a sakamakon Samun sa da laifin taɓa martabar Manzon Allah (S.A.W).