Wata Kotu ta Hukunta Iyaye Matan da ke Tura Ya’yansu Bara

Date:

Wata kotu a Uganda ta yanke wa wasu mata fiye da 100 hukuncin hidimta wa al’umma bayan da suka amsa laifi kan tuhumar da ake musu na tura yaransu bara a Kampala, babban birnin ƙasar.

Kotun ta kuma haramta wa matan komawa birnin tare da bayar da umarnin a tasa ƙeyarsu zuwa mahaifarsu Napak a arewacin Uganda, kamar yadda jaridar Daily Monitor ta ruwaito.

Kotun ta Yanke Hukunci Kan Kalubalantar Hukuncin Kashe Sheikh Abduljabbar

Matan sun nemi a yi masu sassauci inda wasu suka ce sun rasa mazansu, wasu kuma ba sa tare da mazan nasu, in ji jaridar New Vision.

“Na ji kokensu kuma yanke musu hukuncin zaman gidan yari ba zai dace ba. Dole na ɗauki matakin da zai zama wa’azi… Zan yanke musu hukuncin yi wa ƙasa hidima. Idan ka saɓa, za ka yi zaman gidan gyaran hali na wata ɗaya,” in ji alƙalin kotun, Edgar Karakire.

 

Tura yara bara ya saɓa wa dokokin kare ƙananan yara na Uganda kuma laifi ne da ke ɗauke da hukuncin zaman gidan yari na wata shida.

Majalisar Dattawa ta Bayyana Dalilanta na Bincikar Gwamnatin Buhari

An kama matan a watan da ya gabata lokacin da aka ƙaddamar da shirin fatattakar masu bara daga babban birnin gabanin wasu tarukan ƙoli uku na duniya da aka yi a ƙasar.

An kai yaran zuwa wurin rainon yara na Masulita a tsakiyar ƙasar – garin da ke karɓar yaran da aka ceto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...