Babu Isassun Kayan Aikin da Za’a Aiwatar da Ilimi kyauta kuma Dole a Kano – Kungiyar Plane

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Shugabar wata kungiya dake taimakawa ilimin firamare da sakandire a jihar kano PLANE, Hajiya Zainab Isa Ara, ta bayyana cewa ya kamata iyayen yara su san cewa har yanxu ba a fara aiki da tsarin ilimi kyauta kuma dole ba, domin har yanxu babu isason kayan koyu da koyarwar da za’a iya aiwatar da tsarin.

Hajiya Zainab Isa Ara ta bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa tsaki kan harkokin ilimi.

Zainab Isah ta ce har yanxu babu isasun kayan aiki a makarantu a Kano domin haka bai kamata a ce iyaye sun saki jiki da sunan ilimi kyauta ba.

Nijar ta ƙayyade farashin shinkafa a kasar

“Za ku ga wasu iyaye sun aika ya’yansu makaranta babu isassun litattafai babu abun rubutu da sauran kayan koyo a tattare da yaran, wasu ma ko kudin abinci basa baiwa yaransu babu saboda tunanin cewa gwamnati tace ilimi kyauta Kuma dole” .

da yake nasa jawabin, Hon Rabi’u Saleh gwarzo wanda ya wakilci shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar kano (SUBEB), Yusuf Kabir ya ce yayi farin ciki sosai da yadda kungiyar Plane ta ke hubbasa sosai wajen kawo cigaba a bangaren ilimi .

“Hakika ni shaida ne a kan irin abubuwan da plane su keyi a jihar kano da ma kasa baki daya, wanda hadin guiwa ne a tsakanin su da gwamnati hakika zai kawo cigaba. Duk abunda akace akwai cigaba a ciki to dole ne a sami kalubale kuma insha Allahu zamu tabbatar mun isar da sakon su ga gwamnati”. A cewar Rabi’u sale

Majalisar Dattawa ta Bayyana Dalilanta na Bincikar Gwamnatin Buhari

Shi ma a nasa jawabin Garba Adamu mataimaki shugaban kwamitin al’umma gatan makaranta, ya ce idan ana so a kawo karshen matsalolin da ke bangaren ilimi, dole ne a samar da kwamiti da zai kawo hadin kai a tsakanin iyayen yara da malamai makarantu domin a tunkari gwamnati ta idasa abunda a ka kasa cimawwa.

Ya kara da cewa babu wani cigaba da aka samu tun daga lokacin da gwamnati ta fara kirarin ilimi kyauta kuma dole kawo yanxu”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...