Daga Nazifi Bala Dukawa
‘Yan kasuwar masu sayar da magani ta Sabon gari dake jihar kano, ta Umarci’yanta da su rufe shagunan su, har sai abunda hali ya yi, biyo bayan hukuncin wata babbar kotun tarayya a jahar ta yanke, inda ta umarce su, su tashi su koma Kasuwar Dangoro dakea karamar hukumar Kumbotso a jihar kano.
Shugaban yan kasuwar Maganin ta jahar Kano, Musbahu Yahaya Khalid, ya bayyana cewa sun samu kwafin hukuncin kotun da cewar kotun ta kori kararsu, inda yace lauyoyinsu sun shirya tsaf domin daukaka kara.
Sai dai yan kasuwar sun bayyana rashin jin dadin su kan hukuncin kotun, da cewar sun shirya dauka kara, kan yunkurin raba su da sana’arsu.
Iftila’i: Goodluck Jonathan ya Mika Kokon Bararsa ga Yan Nigeria
” korar kara ba sabon abu ba ne ga duk mutumin jihar kano domin gwamnan mu ma an yi masa haka, don haka mu na sa ran idan munje gaba za mu samu nasara”. Acewar Musbahu
Musbaha Yahaya, ya baiwa marasa lafiya hakuri da cewar, lamarin ya faru ne badan suna so ba, sai domin sun sami labarin akwai wasu batagari da suke shirin far mu su shi yasa suka dauki matakin.
Kotu a Kano ta Aike da Ramla Yar TikTok Gidan Yari
” Ma su sana’ar siyar da magani idan sun rasa sana’arnan ba mu san abunda za suje su yi ba. Ya Kamata Mahukunta su duba maganar mu, wurin can da ake kokarin kaimu ba wajen gwamnati ba ne na wasu daban”.
Ya kara da cewa, sun rufe kasuwar don gwamnatin ta san amfanin yan magani a jajar Kano.
” maganar da ake yi cewar yan kabilar Igbo ne ma su sana’ar magani a kano, wannan zance ne marasa tushe, zalinci ne, muna so al’ummar jihar manyan ta da kakana su sani an yi haka ne saboda zalinci.
Sai dai ya ce wajen da ake so a koma ba na gwamnati ba ne, kawai na wasu ne domin tsauwalawa yan kasuwar magani.
Haka zalika yan kasuwar maganin sun yi, sallah tare yin addu’o’in samun nasara a wajen Allah.