Daga Rahama Umar Kwaru
Hukumar da ke Kare Muradan Masu Saye ta Najeriya FCCPC ta sake buΙe katafaren kantin kayar da kayayyaki na Sahad Stores, bayan rufe shi.
A ranar Juma’a 16 ga watan Fabrairu ne hukumar ta garΖame babban kantin, saboda zargin yadda ake cuwa-cuwar sanya farashin kayayyaki a kantin.
Iftila’i: Goodluck Jonathan ya Mika Kokon Bararsa ga Yan Nigeria
Hukumar ta yi zargin cewa masu gudanar da katafaren kantin na Ζara wa abokan hulΙarsu kuΙin kaya fiye da farashin da ke maΖale a jikin kayan.
FCCPC ta ce hakan na tilasta wa kwantomomi biyan kuΙaΙe masu tsada don sayen kayayyaki.
To sai dai cikin wata sanarwa da mai riΖon muΖamin mataimakin shugaban hukumar, Adamu Abdullahi, ya fitar ya ce an sake buΙe kantin domin ci gaba da cinikayya.