Tsadar Rayuwa A Najeriya Ba Laifin Tinubu bane, Ina da Dalili –Khalifa Sanusi II

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya roki ‘yan Najeriya da kada su zargi Shugaba Bola Tinubu da tabarbarewar tattalin arzikin kasar.

Sanusi II ya bayyana cewa ba adalci ba ne a zargi Tinubu kan halin da ake ciki a Najeriya.

Ya zargi gwamnatin da ta shude karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari sakamakon yadda ta tafiyar da kasar .

Dawo da Sanusi Matsayin Sarkin Kano Ba Zai Haifawa Kano Da Mai Ido Ba – Wata Kungiya ga Majalisa

Ya ce gwamnatin Buhari ta yi watsi da shawararsa kan yadda za ta fitar da Najeriya daga matsalolin tattalin arziki.

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana haka ne yayin wani taron addini da aka gudanar a ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu.

Ya ce ’yan Najeriya da suke sa ran zai yi magana game da matsalar tattalin arzikin da kasar ke fama da shi da gangan suka so ya yiwa shugaba Tinubu adawa .

Allah Ya Yiwa Guda Cikin Jaruman Fim din Dadin Kowa Rasuwa

Sanusi ya ce: “Na yi magana a cikin shekarun da suka gabata, game da rikicin da ke gabansa na fuskantar matsalar tattalin arziki. Duk wani masanin tattalin arziki da ya yi nazarin manufofin tattalin arzikin Nigeria a cikin shekaru takwas da suka wuce ya san cewa ‘yan Najeriya za su fada cikin wannan mawuyacin halin.

Halin wahalar rayuwa da ’yan Najeriya ke fuskanta yanzu ma aka fara (idan ba a dauki matakan da suka dace ba) domin Nijeriya ba yar Lele bace, irin wannan yanayi ya faru a Jamus, Zimbabwe, Uganda, da Venezuela.

“Gwamnatin da ta shude ta ki daukar shawarwarin da muka bata a matsayin mu na masana tsarin tattalin arziki. Na fada a gaban shugaban kasa mai ci yanzu a jihar Kaduna, duk dan siyasar da ya ce maka abu zai yi sauki, kada ka zabe shi domin karya yake yi. Mutane sun yi watsi da shawarata”.

“Idan zan yi adalci kuma in yi wa Shugaba Bola Tinubu adalci, ba shi ne ya jawo wahalhalun da ake ciki a yanzu ba; tsawon shekaru takwas, muna rayuwar karya tare da bashi mai yawa daga basusukan waje da na cikin gida. Babban Bankin Najeriya na bin bashin sama da Naira Tiriliyan 30, wanda hakan ya sa bashin ya haura kashi 100 cikin 100.

“Ba zan iya shiga cikin wasu ‘yan Najeriya da ke sukar Tinubu kan matsalar tattalin arziki da ake ciki a halin yanzu ba, kuma ba wai ina cewa shi waliyyi ne da ya kubuta daga aikata ba daidai ba, amma a halin da ake ciki na tattalin arzikin da ake ciki, ba za a zargi Shugaba Tinubu ba. Zan kuma yi magana idan na ga wata manufa ta tattalin arzikin gwamnatin Tinubu a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...

Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Barka da Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447AH

    Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala...

Tinubu zai mayar da Fubara kan kujera gwamnan Rivers amma ya gindaya masa sharadi- Rahoto

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da mayar...

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...