Daga Rahama Umar Kwaru
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayaro yayi kira ga Gwamnatin Tarayya data duba halinda Al’ummar Nigeria suke ciki na tsananin kunci kan hauhawar kayan abinci da rashin zaman lafiya a arewacin Kasar.
Sarkin yayi wannan kira ne a lokacin da Uwar gidan shugaban kasar Nigeria Senator Remi Tuninbu ta ziyarceshi a fadarsa.
Tsadar Rayuwa A Najeriya Ba Laifin Tinubu bane, Ina da Dalili –Khalifa Sanusi II
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren masarautar Kano Abubakar Balarabe kofar Na’isa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya kara da cewa Senator Remi tayi kokari wajan fadada aikinta na alheri da takeyi a jahar kano subada yawan Al umar da jihar kano take dasu.
Allah Ya Yiwa Guda Cikin Jaruman Fim din Dadin Kowa Rasuwa
Datake nata jawabin Uwar gidan Shugan kasar ta bayyanawa sarkin cewa tazo jihar kano ne domin tagodewa Al umar kano bisa goyan bayan da suka bawa mijinta alokacin zabe.
Daga karshe tayi alkawarin isar da sakon al’umar Kano da Arewacin Nigeria ga mai gidannata.
Uwar gidan shugaban kasar Senator Remi Tinubu tasamu rakiyar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa na kasa Senator Barau Jibrin da Gwamnan jihar Benue da matar shugaban majalisar wakilai na kasa da Uwar gidan Gwamnan Kano.