Matasa a Kano na cigaba da yin Zanga-Zanga kan tsadar rayuwa

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Wasu Matasan unguwar gwagwarwa dake karamar hukumar Nasarawa, Kano, sun gudanar da zanga-zangar Lumana domin Mika kokensu ga shugabanni kan tsadar kayan Abinchi da ake fuskanta a Nigeria.

Da yake jawabi ga yan yan jaridu jagoran Matasa da suka gudanar da zanga-zangar a wannan rana ta asabar, Maikudi Boss yace sun gudanar da zanga-zangar ne domin nuna rashin jindadinsu game da halin tsadar kayan Abinchi da ake fuskanta a Nigeria.

” Ya Kamata shugabannin mu su tausawa mana, komai yayi tsada yanzu ya kai Abinchi da mutum zai ci ma ya gagari wasu daga cikin al’umma, don haka akwai bukatar shugabannin a dukkanin matakai su duba matsala da muke ciki” inji Maikudi Boss

Adam A Zango ya Bayyana Dalilan da Suka sa ya Daina Fitowa a Fina-Finan Kannywood

” Muna fama da matsalar tsaro, muna fama da matsalar ta rashin kayan kula da lafiyarmu a asibitocin ga talauci yayi mana yawa, kuma a mulkin dimokaradiyya gwamnatin da mu muka zabeta da hannayenmu, Gaskiya ya kamata shugabannin mu ku ji tsoron Allah ku tausaya mana”.

Rundunar Yan Sandan Kano ta Bayyana Shirin ta Kan Ziyarar Matar Tinubu

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito tun a ranar litinin din data gabata rukunonin Matasa daban-daban a jihohin Kano Neje da Kogi suke ta gudanar da zanga-zangar lumana domin Mika kokensu ga shugabanni don su dauki matakan da suka dace don saita al’amuran.

Ko tsakiyar wannan makon mai karewa sai da shugabannin kasa ya gudanar da wani taron gaggawa da masu ruwa da tsaki musamman a sha’anin samar da Abinchi, kuma yayi alkawarin fito da hatsi daga babban rumbun kasa don samar da isashen Abinchi ga al’ummar Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...