Rundunar Yan Sandan Kano ta Bayyana Shirin ta Kan Ziyarar Matar Tinubu

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta tabbatar da cewa ta shirya tsaf ta fuskar samar da tsaro domin ziyarar aiki da uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta kai jihar a ranar 12 ga watan Fabrairu.

Kwamishinan ‘yan sandan, Hussaini Gumel, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a Kano.

Gumel ya ce sun samar da isassun jami’an tsaro wadanda suke cikin shiri domin tabbatar da uwar gidan shugaban kasa ta kammala ziyarar da zata kawo kano lami lafiya .

Tsadar Rayuwa: Abubuwan da Ɗangote yayi alkawarin taimakawa al’ummar Kano da su

Gumel ya ce rundunar ta dauki kwararan matakan tsaro domin tabbatar da ziyarar lafiya.

“Mun tattara isassun jami’ai masu dauke da makamai domin baiwa uwargidan shugaban kasa kariya kafin ziyarar, da lokacin da kuma bayan ziyarar,” in ji Gumel.

Kwamishinan ya kuma ce tuni rundunar ta fara shirin “Operation Show Force” tare da sauran jami’an tsaro domin nuna shirin su kan ziyarar uwar gidan.

Tinubu Ya Bayar da Sabon Umarni ga Yan Nigeria

Ya bayyana cewa an dauki matakan ne domin baiwa mazauna jihar damar tarbar uwargidan shugaban kasar da mukarrabanta ba tare da wata barazana ta tsaro ba .

Kwamishinan ya shawarci shugabannin jam’iyyun siyasar jihar da su ja hankalin magoya bayansu da su nisanci duk wani nau’in tashin hankali da ‘yan daba kafin ziyarar uwargidan shugaban kasa da kuma bayan ziyarar.

Gumel ya ce: “Ba za mu amince da duk wani aiki da zai kawo rudani kafin ziyarar, lokacin da kuma bayan ziyarar ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...