Kotu a Kano ta buƙaci a yi wa Hafsat Chuchu gwajin ƙwaƙwalwa

Date:

Wata babbar kotu da ke zaman ta a birnin Kano ta buƙaci a yi wa Hafsat Surajo (Chuchu) gwajin taɓin hankali a ci gaba da shari’ar da ake yi mata kan zargin kisan wani matashi mai suna Nafi’u Hafiz.

Kotu ta ɗauki wannan mataki ne bayan da Hafsat ta ƙi cewa uffan a lokacin da aka karanta mata tuhumar da ake yi mata.

Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Zuwaira Yusuf ta buƙaci a samu likitan ƙwaƙwalwa da zai duba lafiyar Hafsat a inda ake tsare da ita.

Da dumi-dumi: Kungiyar Kwadago ta Bayyana Ranar Fara Yajin Aiki a Nigeria

Tun farko an karanta wa Hafsat laifukan da ake tuhumar ta da su, sai dai ba ta ce komai ba a lokacin da kotu ta tambaye ta ko ta fahimci abin da ake nufi ko a’a, balle ma ta amsa ko tana da hannu a cikin abin da ake zargin nata da shi ko a’a.

Yanzu haka kotun za ta jira sakamakon gwajin da likita zai yi wa Hafsat kafin ci gaba da sauraron shari’ar.

A cewar kotu, dole ne a tantance lafiyar duk wanda ake tuhuma kafin ci gaba da shari’a, kasancewar “ba a yin shari’a da mai taɓin hankali.”

Wannan ne karo na farko da ake karanto wa Hafsat tuhume-tuhumen da ake yi mata a gaban babbar kotun.

Jinkirin biyan albashi: Ma’aikatan gwamnati sun kalubalanci Tinubu

An gabatar da ita ne a kotun tare da mijinta da kuma wasu mutum biyu da ake zargi da hannu wajen aikata laifin.

Haka nan a lokacin zaman na yau Alhamis, lauyoyin waɗanda ake tuhuma sun gabatar wa kotu buƙatar bayar da belin mjin na Hafsat da sauran mutum biyun, sai dai kotun ta ce za ta sanya ranar sauraron buƙatar tasu.

A watan Disamban shekarar da ta gabata ne rundunar ƴansanda a jihar Kano ta bayyana cewa jami’anta sun kama Hafsat Surajo ƴar shekara 24 da ke Unguwa Uku bisa zargin kashe Nafi’u Hafiz, ɗan shekara 38 a gidanta na aure.

Haka zalika binciken ƴansandan ya kai ga kama mijin matashiyar, Dayyabu Abdullahi mai shekara 38, sai kuma Mallam Adamu mai shekara 65 da kuma ƙarin wani mutum ɗaya.

Tun a wancan lokaci ne kotu ta bayar da umarnin ajiye Hafsat a gidan kaso.

Bayan kammala zaman kotun na yau an mayar da Hafsat da sauran waɗanda ake tuhuma zuwa gidan gyaran hali domin ci gaba da tsare su.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Aminu Dantata ya bar mana wasiyyar inda za a binne shi – Iyalansa

Iyalan marigayi Alhaji Aminu Alassan Dantata sun shaida cewa...

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...

Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Barka da Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447AH

    Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala...

Tinubu zai mayar da Fubara kan kujera gwamnan Rivers amma ya gindaya masa sharadi- Rahoto

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da mayar...