An Dakatar Da Lakcara Saboda Sa Dalibai Gwale-Gwale A Kano

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil a Jihar Kano ta dakatar a wani malaminta kan sa dalibai gwale-gwale.

Jami’in Hulda da Jama’a na jami’ar, Sa’idu Nayaya, ya sanar a ranar Laraba cewa an dakatar da malamin ne sakamakon wani bidiyonsa da ya karade kafofin yada labarai.

Gobara ta Kone Kayan Abinchi da Dabbobi a Kano

A cikin bidiyon an ga malamin yana sa dalibai gwale-gwale a cikin aji saboda sun makara, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce da kiraye-kirayen neman taka masa burki.

Mun Dukufa Neman Hanyoyin Magance Tsadar Kayan Abinchi a Nigeria – Tinubu

“Hakan ne ya sa aka dakatar da shi nan take aka mika lamarin ga kwamitin ladabtarwa na manyan malamai domin daukar matakin da ya dace.

“Hakan zai tabbatar da adalci da kuma hana sake faruwar irin haka a nan gaba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Alhaji Aminu Dantata ta bar gibin da zai yi wuyar cikewa a Nigeria – Alhaji. Kabiru Sani Kwangila

Shugaban kamfanin gine-gine na SKY Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Sanarwa ta Musamman daga majalisar malaman Kano game da rasuwar Dantata

SANARWA MUHIMMIYA (GABATAR DA SALLATUL GA'IB) Assalamu Alaikum Warahmatullah, Sakamakon rasuwa...

Aminu Dantata ya bar mana wasiyyar inda za a binne shi – Iyalansa

Iyalan marigayi Alhaji Aminu Alassan Dantata sun shaida cewa...

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...