Daga Isa Ahmad Getso
Wasu sojoji sun harbe wani soja mai suna James Kingsley bayan da ya yi harbi da bindiga wanda ya yi sanadin mutuwar babban jami’insu.
Wannan mummunan al’amari ya faru ne a sansanin ‘Forward Operational Base’ da ke Magami a Sakkwato, a karkashin rundunar hadin gwiwa ta Operation HADARIN DAJI (OPHD).
INEC ta Bayyana Sakamakon Yan Majalisun Jihar Kano Guda biyu
Babban jami’in da aka kashe, mai mukamin Second Laftanar mai suna OC Ukachuckwu (N/19548), ya rasa ransa ne a lokacin da lamarin ya faru a ranar Lahadi da karfe 6:05 na yamma.
NAHCON ta Bayyana Yadda Saudiyya Ta Rage Kudin Aikin Hajjin Bana
A cewar wata majiyar daga cikin sojojin, Kingsley ya bude wuta, inda ya kashe Ukachuckwu, kafin daga bisani wasu sojojin da ke wurin su kashe shi .
Wasu daga cikin abokan aikin Kingsley sun samu raunuka a yayin da lamarin ya faru amma an ruwaito cewa suna samun kulawar likitoci a asibiti.
Daily Post