Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bada sanarwar soke dakatar da zaben dan majalisar jihar da Ake sakewa a yankin kananan hukumomin Kunchi da tsanyawa a jihar Kano.
“Mun dakatar da zaɓen da yake gudanar yanzu haka a mazabu goba na karamar hukumar kunchi sakamakon yadda yan daba suka lalata kayan aikin zaɓen”.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan hulda da Jama’a da wayar da kan masu zaɓen na hukumar Sam Olumekun ya sanyawa hannu .
Zaben Cike Gurbi: INEC ta Magantu Kan Sace Akwatunan Zabe a Kano
Sanarwar tace matakin dakatar da zaɓen yayi daidai da sashi na 24 (3) na dokar zabe ta 2022. “zamu sanar da mataki na gaba da zamu dauka bayan gama ganawa da masu ruwa da tsaki na hukumar a ranar litinin”.
Sanarwar dakatar da zaɓen ta shafi zaɓen da ake gudanar a wasu mazabu a jihohin Akwa Ibom da Enugu.
INEC ta kuma bukaci jami’an tsaro da su gudanar da bincike kan lamarin, yayin da ta ce ita na zata gudanar da bincike don tabbatar da ko akwai sakacin ma’aikatan ta