Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Hukumar gudanarwar rukunonin kamfanonin Ɗangote ta yi bayani dalla-dalla dangane da dalilan da suka sanya hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta ziyarci Ofishin Kamfanin Ɗangote dake jihar Legos a ranar 4 ga watan janairun shekara ta 2024.
“A ranar 6 ga watan Disamba,2023 mun samu wasika daga Hukumar Yaki da Cin Hanci da rashawa ta kasa wato
EFCC, inda suke bukatar mu basu ba’asin Kudaden waje wato Dalar Amurka da Babban Bankin Najeriya ya bamu
daga shekara 2014 zuwa yanzu. Mun fahimci cewa ba mu kadai aka baiwa wannan wasikar ba, an turawa wasu
kamfanonin kimanin 51 irin wannan wasikar kuma suma ana neman wannan bayanin daga gare su”.
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar gudanarwar rukunonin kamfanonin Ɗangote ta sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.
Sanarwar ta ce “Mun baiwa Hukumar EFCC takardar karbar bukatar da suka turo mana, muka kuma bukaci su yi mana karin bayani a bangaren da suke bukatar bayanin, ko kuma daga wane bangare na rukunin kamfanonin mu. Mun kuma bukaci karin lokaci domin hadawa tare da gabatar musu takardun da suka kai shekaru goma.
“Haka Kuma, hukumar EFCC basu fayyace mana bangaren da suke da bukatar bayanan ba, kuma basu bamu
damar da muka bukata daga gare su ba dangane da karin lokaci, suka kafe akan lallai suna da bukatar wannan
bayanai a kurarren lokaci. Duk da wannan ‘sa toka sa katsin’ da akayi, mun tabbatarwa hukumar EFCC cewa
zamu gabatar musu da bayanan da suka bukata a lokuta daban da ban saboda muna kan kamala tattara
bayanan”. A cewar Kamfanin Ɗangote
Gaskiyar Batu Kan Ranar Yanke Hukuncin Shari’ar Gwamnan Kano
Sanarwar ta kuma kara da cewa “A ranar 4 ga watan janairu 2024, ma’aikatan mu suka fara mikawa Hukumar EFCC rahoto kashi na farko. Baya ga haka, Jami’an hukumar EFCC suka ki karbar takardun rahoton da muka gabatar musu, suka ki amincewa da kai musu da akayi, suka ce sai dai su zo ofishin mu su karbi wannan kwafin rahoton da muka gabatar musu da kansu.
“Duk da kasancewar ma’aikatan mu suna ofishin su da takardun bayanan da suka bukata, wasu daga cikin
jami’ansu suka wuce zuwa ofisoshin domin karbar wannan rahoton da aka gabatar musu wanda hakan ya zubar
mana da kima da kuma taba darajar mu. Duk da yake jami’an nasu basu dauki wasu takardu ko kuma wani kundi
daga ofishin namu ba a lokacin zuwan nasu, domin duk abinda suke nema yana ofishin su”.
Dan Jaridar Da Ya Tona Asirin Digirin Dan Kwatano Ya Koka
“Muna fada da babbar murya cewa, babu wani zargi ko kuma wata badakala da ake zargin daya daga cikin
rukunin kamfaninnikan mu da ita a wannan lokacin, face dai muna bayar da bayanan da aka bukata daga gare
mu domin taimakawa hukumar EFCC a binciken da take yi”. Inji Ɗangote
“A matsayinmu na kamfanin da yake biyayya ga dokokin kasa, a shirye muke da mu bada hadin kai wajen baiwa
hukumar EFCC duk wani bayani da suke da bukata daga wajen mu. Mun riga mun mika musu kason farko na
bayanan da suka bukata daga gare mu, muna kuma aiki tukuru domin ganin mun basu sauran bayanan da suka
rage daga gare mu akan lokaci, domin taimakawa binciken da suke yi”.
Sanarwar ta ce “Gamaiyar Kamfanonin mu suna daga cikin wadanda suka fi bada gudunmawa wajen bunkasar tattalin arzikin kasar nan, kuma daya cikin manyan kamfanonin dake kasuwar hanneyen jarin kasar nan, sannan kuma daya daga cikin manyan kamfanonin da suka fi biyan haraji mai yawa a kasan nan. Mun kasance masu biyaiya ga
dokin kasa tare da kare martabar ta a yunkurin da gwamnatin taraiya take yin a ganin an samar da bunkasar
tattalin arziki ta yanda masu zuba hannayen jari na gida dana waje zasu sami damar yin hakan”.
Kamfanin na Ɗangote ya yi kira ga abokan huldarsu su fahimci yanda abin yake, su kuma kwantar da hankalin su. Zasu ci gaba da sanar dasu duk halin da ake ci lokaci zuwa lokaci.