Wata Kotu a Kano Ta Janye Umarnin kamo Wani Jami’in Kwastam

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Tun bayan da Alkalin Babbar kotun shari’ar Addinin Musulunci dake zamanta a sabon gari a jihar Kano, Mai shari’a Hamza Garba Malafa ya bada Umarnin a kamo wani jami’in costom mai suna Yusuf Isma’il Mukhtar mai Biscuit, biyo bayan kin bayyana a kotun tun a ranar Alhamis din data gabata.

Sai dai lauyan wanda ake kara Sani Idris ya bayyanawa manema labarai cewa wanda ake kara tun da farko ba’a bashi sammaci hannu da hannu ba, Amma bisa sanin darajar kotu ya tura lauya kotu tunda sanyin safiya har zuwa 12:00pm, don Jin bahasi.

Talla

Da yake bayyana yanda suka samu cewa ankai wa wanda ake kara sammaci, Sani Idris lauyan wanda ake kara, yace kanin wanda ake kara akai kaiwa takardar sammacin bayan anje gidansu baya gida, Shi kuma kanin daya gani ya tabbatar daga kotu ne, ya shaida wa yayan Bashir don haka shi kuma wanda ake kara ya tura lauya don girmama kotu.

Kazalika lauyan mai kara ya bayyana cewa, duk wani mai damara ba’a bashi sammaci kai tsaye ko kuma bada oda a kamo shi, sai dai a turawa ma’aikatar da yake aiki cewa ana shari’a dashi a bashi dama zuwa kotun da shari’ar ke gudana.

Gaskiyar Batu Kan Ranar Yanke Hukuncin Shari’ar Gwamnan Kano

Yace shi Kwastam din da ake kara yana aiki ne a shelikwatar hukumar dake jihar lagos, idan ba’a Aika legas ba to kyautuwa yayi a Aika Babbar shelikwatar Kwastam ta kasa gaba daya a bukace shi kan laifin da ake kararsa akai, sannan a bashi damar zuwa kotu cewar lauyan Wanda Ake Kara Yusuf Ismail Mukhtar, Amma duk ba’ayi haka ba kuma duk da haka yana biyaya ga kotu don haka ya dauki matakin daukar lauya.

Sanya Ministar Jin Kai Better Edu cikin badakalar NSIPA da EFCC ke bincike rashin adalci ne – Arewa Integrity Group

Lauyan wanda ake kara Sani Idris ya kara da cewa Sam ba’a bi tsarin sharia bane yanda suke kwallo kuma anyi haka ne Domin a batawa Wanda Ake kara suna, don haka suka nusar da kotu ta Ajiye odar data bayar a Baya.

Yanzu haka Alkalin kotun Mai shari’a Hamza Garba ya bada Umarnin a koma kotu ranar 8/01/24, bayan Ajiye waccen order dake Umarnin a kamo Wanda Ake Kara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...