Sanya Ministar Jin Kai Better Edu cikin badakalar NSIPA da EFCC ke bincike rashin adalci ne – Arewa Integrity Group

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Wata Kungiya dake rajin ganin an yaki cin hanci da rashawa a Nigeria mai suna Arewa Integrity Group, ta bukaci hukumar EFCC da kada ta saurari masu kiraye-kirayen shigar da Ministar ma’aikatar jin kai da kawar da talauci ta kasa Dr. Better Edu cikin binciken da take yi kan badakalar hukumar NSIPA.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito shugaban Kasar Bola Ahmad Tinubu ya amince da dakatar da Shugabar hukumar NSIPA Hajiya Halima shehu kan badakalar karkatar da Naira Biliyan 44.8 na hukumar zuwa wani asusu na daban.

Kadaura24 ta rawaito, shugaban kungiyar Arewa Integrity Group Alhaji Ibrahim Sambo ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a ranar asabar.

Talla

“Muna matukar farin ciki da yadda gwamnati ta sanya hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gudanar da bincike kan bacewar biliyoyin naira daga wannan hukuma da aka kafa domin rage radadin talauci a tsakanin al’umma”.

Kungiyar Arewa Integrity Group tace tana cikin fargabar cewa, maimakon a bar binciken gwamnatin tarayya ya ci gaba da tafiya ba tare da tangarda ba, an yi wani shiri da aka tsara don haifar da hargitsi a ma’aikatar baki daya.

Gaskiyar Batu Kan Ranar Yanke Hukuncin Shari’ar Gwamnan Kano

Wannan makirci ne da ake amfani da kafafen yada labarai wajen ganin an jawo Ministar ma’aikatar jin kai, Dr. Betta Edu cikin rudani na zargin karkatar da Naira biliyan 44.8 daga asusun NSIPA”.

” A matsayinmu na kungiyar Integrity da aikin mu ya yi daidai da matakin da gwamnatin tarayya take dauka na yaki da cin hanci da rashawa, muna goyon bayan binciken da EFCC ke yi, muna fata za’a kamo duk masu hannu a cikin badakalar a kuma hukunta shi kamar yadda doka ta tanada”.

Alhaji Ibrahim Sambo ya kara da cewa, sun lura da ayyukan jami’an gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, sun kuma tabbatar da cewa Dr Betta Edu na daya daga cikin wadanda suka samu nasara a aikin da aka dora musu. wannan ne ya sa suka firgita a kan kiraye-kirayen da wasu yan tsiraru ke ganin an sanya girma minista a cikin binciken badakalar NSIPA da EFCC ke yi.

Ministar Abuja Mariya Bunkure ta fita zakka cikin masu mukaman gwamnatin tarayya a Kano – Hon. Abba Kawu

” Muna da bukatar yin magana da kare mutuncin wannan minista mai aiki tukuru, don nuna jin dadinmu ga duk kokarin da ta yi da kuma tabbatar wa sauran wadanda suka samu nasarori a gwamnati cewa mu al’umma za mu ba su goyon baya a kodayaushe a lokacin da miyagu suke kokarin far musu ta hanyar bata musu suna”. A cewar Sambo

Binciken mu ya gano cewa kiraye-kirayen a jawo Dr Edu cikin badakalar biliyoyin Naira na NSIPA ya samo asali ne daga karya da gangan da kuma karya da nufin karkatar da hankalin hukumar EFCC daga aikin da take yi kan wadanda ake zargi da karkatar da wadancan Kudade”.

“Muna amfani da wannan damar wajen gargadin dukkan masu wadancan rubuce-rubuce da masu daukar nauyinsu cewa ba za mu zubar idanu a banza ba yayin da suke neman kawo cikas ga kokarin gwamnati na samar da tallafi ga masu karamin karfi ‘yan Najeriya da kuma fitar da talakawa miliyan 50 daga kangin talauci a cikin watanni 42 daidai da ajandar sabunta kasa ta Shugaba Tinubu. .

“Muna fata nan ba da jimawa ba binciken EFCC zai ba da amsoshi ga muhimman tambayoyin da tsohuwar kodinetan NSIPA ya kasa ta cire Naira biliyan 44.4 daga asusun gwamnati tare da karkatar da wasu asusu na sirri daban-daban” inji Ibrahim Sambo

Shugaban Kungiyar Arewa Integrity Group Alhaji Ibrahim Sambo ya kuma ce suna yaba wa Dr Edu bisa jagorancin kawo gyara a ma’aikatar cikin kankanin lokaci tare da yin kira ga ma’aikatan ma’aikatar da su hada kai da ita domin cimma manyan manufofin ma’aikatar na kawar da talauci a tsakanin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...